Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta ci tarar dala 5,000 ga tawagar kasar Masar bayan ta yi ki bada dama wa kafofin watsa labarai a wasan farko da ta yi da Zimbabwe 2-1 a gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2025,
A cewar CAF, an yanke hukuncin ne bayan da ‘yan wasa da masu horaswa na Masar suka kasa bin ka’idojin hira da yan jarida na bayan wasa.
An ruwaito cewa dukkan tawagar Masar sun yi tafiyasu ba tare da kulla ‘yan jarida ko amsa duk wata tambaya bayan wasa ba, matakin da CAF ta bayyana a matsayin keta dokokinta na kafofin watsa labarai.
CAF ta kuma yi gargadi a hukumance ga zakarun Afirka sau bakwai, tana mai jaddada cewa za a aiwatar da hukunci mai tsauri idan aka sake maimaita karya dokar.
Hukumar nahiyar ta yi gargadin musamman cewa za a dauki karin hukunci idan Masar ta kasa cika kaidojin na kafofin watsa labarai bayan fafatawa da Afirka ta Kudu a ranar juma’a
Hukuncin ya jaddada ci gaba da kokarin CAF na aiwatar da dokokin samun damar ga kafofin watsa labarai a gasar, wanda aka tsara don inganta bayyana gaskiya da kuma inganta yada labaran gasar cin kofin kasashen Afirka.


