CAF Ta fara Bincike Kan Rikicin Bayan tashi a Wasan Algeria Da Najeriya.
Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta fara bincike a hukumance kan munanan abubuwan da suka biyo bayan wasan kwata-final na Kofin Kasashen Afirka tsakanin Algeria da Najeriya a daren Asabar,
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, CAF ta tabbatar da cewa ‘yan wasan Algeria da membobin ma’aikatan bangaren masu horaswa sun tunkari alkalin wasan jim kadan bayan an busa tashi a wasan.
An ruwaito cewa lamarin ya kara kamari yayin da wasu daga cikin ‘yan wasan Algeria suka bi alkalan wasa zuwa cikin hanyar tafiyarsa zuwa dakin hutawa da aka tanadar masa, wani abu da CAF ta kira “abin da ba za a yarda da shi ba” kuma ya saba wa dokokin ladabtarwa na gasar.
CAF ta kuma bayyana cewa tana duba rahotannin rikicin da ya shafi ‘yan jarida da sauran ma’aikatan kafofin watsa labarai bayan tashi a wasan, yayin da tashin hankali ya bazu a wajen filin wasa.
Wasan Algeria da Najeriya, wanda aka buga a Marrakech, ya ƙare da 2-0 nasara ga Super Eagles, ta Najeriya sakamakon da ya haifar da yanayin hayaniya daga sansanin Algeria.
Hukumar ta tabbatar da cewa za a yi nazari sosai kan dukkan rahotannin wasanni, na gabatar da alkalan wasa, da kuma shaidun bidiyo a matsayin wani bangare na binciken.
CAF ta kara da cewa za a sanar da matakan ladabtarwa da suka dace da zarar an kammala binciken.
Wannan lamari na ci gaba da kara haifar da cece-kuce a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Afirka, yayin da AFCON 2025 ke shirin shiga mataki mai muhimmanci na wasan dab da karshen.


