Gombe Ta Yi Gasar Makarantun Firamare Don Bikin Cika Shekaru 100 Na Hassan Central
Makarantar Firamare ta Herwagana ta lashe kofin gasar ƙwallon ƙafa ta makarantun firamare da aka shirya domin bikin cika shekaru 100 da kafuwar Makarantar Firamare ta Hassan Central da ke Gombe. An gudanar da wasan ƙarshe na gasar a Filin Wasan Pantami, inda Herwagana ta doke Hassan Central da ci 4–3 ta hanyar bugun fenariti…

