Kungiyar Barcelona ta sha dukkan kawo-wuka a hanun Chelsea.
A ranar Talata 25 ga watan Nuwamban 2025 aka fafata a gasar cin kofin Zakarun Nahiyar Turai UCL, na shekara 2025/26, kungiyoyin kwallon kafa na turai 18 ne suka gwabza a tsakaninsu.
Inda ƙungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta lallasa Barcelona da ci uku da nema 3-0. Dan wasan Barcelona mai suna Jules Oliveir Kounde, shi ne ya sha gida a minti na 27 kafin tafiya hutun rabin lokaci, bayan dawo daga hutun rabin lokaci kuma dan wasan Chelsea Estevao, ya zura kwallo ta biyu a ragar Barcelona a mintina na 55, daga bisani a mintuna na 73 Liam Delap, ya jefa kwallon ta uku haka dai aka tashi a wasan Chelsea na da kwallo 3-0.
A sauran wasannin da aka buga kuwa.
Ajax 0-2 Benfica
Galatasaray 0-1 Union Saint-Gilloise
FK Bodø / Glimt 2-3 Juventus
Borussia Dortmund 4-0 Villarreal
Manchester City 0-2 Bayer Leverkusen
Marseille 2-1 Newcastle United
Napoli 2-0 Qarabağ
Slavia Praha 0-0 Athletic Club
Ajax 0-2 Benfica
A Yau kuma za’a gwabza a gasar ta cin kofin Zakarun Nahiyar Afirka UCL 2025/26
Ƙungiyar kwallon kafa ta Arsenal a gida suna tare da Bayern Munich.
Pafos da Monaco da misalin karfe bakwai saura kwata agogon Najeriya
Kobenhevm da Kairat Almaty
Olympiacos da Real Madrid
Liverpool da PSG
Athletico da Inter Milan
Frankfurt da Atlanta
Sporting CP da Club Brugge
Wayannan wasan za’ayi sune da misalin karfe tara agogon Najeriya Nijar Kamaru da Chadi karfe 8 agogon GMT da Ghana.


