Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Dakarun Sojin Amurka Sunfara Sauka A Najeriya
Published: February 17, 2026 at 7:02 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kimanin sojojin Amurka 100 ne suka isa Najeriya, yayinda hukumomi a Washington suke karfafa matakan yaki da ‘yan bindiga masu ra’ayin jihadi, kamar yadda kakakin sojojin Najeriya ya fada.

Amurka ta kaddamar da hare hare kan ‘yan tawayen da suke ikirarin musulunci cikin watan Disamba, yanzu kuma wata ‘yar tawagar sojojin Amurka suna aiki cikin kasar domin su taimakawa sojojin Najeriya wajen tattara bayanan sirri.

A cikin ‘yan kwanakin nan jiragen sama masu yawa dauke da sojojin Amurka da kayan aiki suna isa jihohin dake arewacin kasar, kamar yadda bayanai daga wani dandali dake sa ido kan zirga zirgan jiragen sama ya nuna, da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani.

Kamar yadda kakakin helkwatar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Sama’ila Uba ya fada, dakarun na Amurka za su horasda sojin Najeriya tare da ba su shawarwari, amma ba za su je fagen daga ba.

Tun a farkon watan nan, rundunar sojin Najeriya tace ta na saran kimanin sojojin Amurka 200 za su isa kasar.

Ahalinda ake ciki kuma, ofishin kididdiga ta Najeriya ta fada jiya litinin cewa hauhawar farashin kayayyaki ya ragu a watan Disemban bara, daga 15.15 yanzu ya sauko zuwa kashi 15.10, wanda ya nuna saukar ko raguwar tsadar kayayyaki watanni 10 a jere.

Amurka, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Ministan Harkokin Wajen Iran Yagana Da Shugaban Sa’ido Akan Nukiliya
Next Post: ‘Yan Tawaye A Burkina Faso Sun Kashe ‘Yan Kasar Ghana

Karin Labarai Masu Alaka

Kungiyar Kwadago Ta Shirya Zanga-Zanga A Najeriya Najeriya
Tarkacen Makamai Masu Linzami Sun Lalata Gidaje Da Wuraren Kasuwancin Palasdinawa Afrika
Akwai Nasara A Tattaunawar Da Akeyi Tsakanin Iran Da Amurka Afrika
Domin Karfafa Tsaro Babban Hafsan Sojin Najeriya Ya Ziyarci Jos Afrika
Yeriman Ingila Ya Gana Da Yeriman Saudiya Mai Jiran Gado Amurka
An Yi Fashin Kaguwa Da Dodon-Kodi Na Miliyoyin Dalar Amurka Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Amurka Ta Janye Sojojinta Daga Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Sojoji Sunkai Farmaki Gidan Dan Adawa A Kasar Uganda Bobi Wine Afrika
  • Rikici Tsakanin NNPC Da Kungiyar Gwamnoni Akan Gibin Kudade Labarai
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Turkiyya Tana Gudanar Da Binciken Kasar Da Suka Kona Tutar Ta Tsaro
  • Wani Bayahude Ya Harbe Bafalatsine Dan Shekaru 16 Tsaro
  • Amurka Tace Zata Gama Yakin Iran Cikin Makonni Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Tana Saka Ido Akan Matsalolin Gabas Ta Tsakiya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.