Babban Hafsan Sojin Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, a ranar Alhamis 2 ga Afrilu, 2026, ya jagoranci shugabannin hukumomin tsaro domin duba halin tsaro kai tsaye a birnin Jos na jihar Filato
Mukaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Soji, Kanal Appolonia Anele, ta bayyana a wata sanarwa cewa ziyarar na daga cikin ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da tabbatar da dorewar sa a faɗin jihar.
Sanarwar ta ce, bayan isowarsa ya samu tarba daga gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, a matsayin alamar kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin farar hula da sojoji wajen magance matsalolin tsaro.
Haka kuma, COAS ya karɓi cikakken bayani kan ayyukan tsaro daga Babban Kwamandan Runduna ta 3 da kuma Kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta Operation ENDURING PEACE, Manjo Janar Folusho Oyinlola, wanda ya yi bayani kan matakan da ake ɗauka tare da sauran hukumomin tsaro domin dakile barazana, kare rayuka da dukiyoyi, da kuma daidaita al’ummomin da abin ya shafa.
A yayin ziyarar, Laftanar Janar Waidi Shaibu ya gana da shugabannin al’umma da mazauna yankin, inda ya tabbatar musu da ƙudirin rundunar sojin kasa ta Najeriya na kare rayukan dukkan ‘yan ƙasa masu bin doka.
Ya kuma buƙaci al’umma su kasance cikin natsuwa da taka-tsantsan, su kuma mara wa hukumomin tsaro baya ta hanyar bin dokar takaita zirga-zirga (curfew) da kuma ba da cikakken haɗin kai a ayyukan bincike da tsaro, yayin da suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Shugaban ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, Mr. Dachung Bagos, ya yaba da ziyarar COAS, yana mai cewa zuwan manyan shugabannin soji zai ƙara wa jama’a kwarin gwiwa tare da ƙarfafa amincewa da matakan tsaro da ake ɗauka.


