Farashin danyen mai ya farfado da fiye da kashi daya cikin dari a yau laraba, bayanda shugaban Amurka Donald Trump, ya bada umarnin hana jiragen dakon mai da aka azawa takunkumi shiga ko fita daga Venezuela, al’amarii da ya kara jefa zaman dar dar ta fuskar siyasa a duniya, kuma ya rage fargabar da ake yi cewa kasuwar mai zata yi kwante.
Mai da ake kira Brent ya tashi da kashi daya da digo 68, watau dala 59 da kobon Amurka 91, yayinda mai da ake kira West Texas ya karu da kashi fiyeda daya d rabi, ya tsaya kan kudi dala 56 da centi ashirin kan ko wace ganga.
Yawan mai da Amurk take hakowa ya hana farashin mai tashi a kasuwannin duniya.
Farashin mai yayi kasa sosai da rabon aga haka kamar shekaru biiyar da suka wuce, kan tsammanin za’a sami dai dato kan yakin Rasha da Ukraine, mataki da zai sa a dage takunkumin da aka kakabawa Rasha, hakan zai rage farashin mai, yayinda kasuwar mai take nuna rashin tabbas


