Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Farashin Mai A Kasuwannin Duniya Yayi ƙasa Kadan
Published: January 1, 2026 at 9:40 AM | By: Bala Hassan

Farashin mai a kasuwannin duniya yayi kasa kadan, waddaa yake nuna farashin mai yayi kasa da kamar kashi 15 cikin dari a shekaran nan da ta kare, saboda zaton za’a sami  kwantai, sakamakon   karin haraji kan cinikayya, karin mai da kunigyar kasashe masu arzikin mai OPEC suke fitarwa, da kuma takunkumin da aka azawa Rasha, da Iran, da kuma Venezuela.

Ahalinda ake ciki kuma, akalla jiragen ruwa masu dakon mai 2 sun isa Venezuela a cikin ‘yan kwanakin nan, yayinda wasu jiragen suka doshi can, a wani yunkurin da hukumar kula da harkokin mai na kasar take yi na fadada adana da kuma ci gaba da sayarda mai, duk da matakin killace kasar ta ruwa da Amurka take yi, wadda ya rage yawan mai da kasar take fitarwa.

A cikin wancan shekarar ne shugaba Donald Trump na Amurka ya bada sanarwar hana jiragen ruwa mas dakon mai da aka azawa takunkumi shiga ko fita daga Venezuela, a wani mataki na kara matsin lamba kan shugaba Maduro na kasar. Matakinda Amurkan ta dauka ya rage yawan mai da kasar Venezuela take sayarwa kamar da rabin abunda kasar ta fitar cikin watan Nuwambar 2025.

Amurka ta kama jiragen ruwa biyu wadanda suke cike makil da mai daga Venezuela, yayinda kuma jiragen ruwanta suna siintiri a tekun dake yankin na Carribean. Wannnan mataki ya tsorata masu jiragen dakon mai masu yawa, jirage kalilan ne suke zuwa kasar ta Venezueala wacce memba ce a kungiyar kasashe masu arikin mai watau OPEC.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Farashin Gangar Mai Yayi Gagarumar Fadi A Kasashen Duniya
Next Post: Putin, Sakon Sabuwar Shekara Ya Jinjinawa Dakarun Rasha Da Suke Yaki A Ukraine

Karin Labarai Masu Alaka

Yau Shekaru 60 Da Kisan Gilla Ga Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Musa: “Da Yaddar Allah Zamu Ga Bayan Ta’addanci A Najeriya” Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Zamfara: Sai Mun Hada Kai Don Kawo Karshen Ta’addanci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Ga Watan Ramadan A Najeriya Da Nijar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Christ Musa Ministan Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Samar Da Tsaro A Jihar Kano Ba Sai An Sa Siyasa Ba! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Abba Kabir Yusuf Ya Koma Jam’iyar APC Siyasa
  • Ganduje Ya Nisanta Kansa Da Batan Dadiyata Labarai
  • Gwamnatin Tarayya Ta Samu Nasarar Ceto Wasu Daliban St. Mary’s Tsaro
  • Dalibin Jami’a Ya Rasa Ransa A Birnin Dakar Yayin Zanga Zanga Afrika
  • Amurka Zata Bada Gudunwa Ga Masu Zanga-Zanga A Iran Sauran Duniya
  • Shugaba Trump Yace Amurka Ce Zata Rika Gudanar Da Harkokin Kasar Venezuela Amurka
  • An Bude Kamfanin Sarrafa Ma’adanai A Kasar Mozambique Labarai
  • Gwamnatin Soji A Nijar Ta Hana Fitar Da Albarkatun Kasa Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.