Akalla mutane 10 ne suka mutu, wasu da dama kuma sun jikkata a wani mummunan hadarin mota da ya afku a kan hanyar Jama’are zuwa Azare a kan titin Kano zuwa Maiduguri, inda wata motar haya ke dauke da fasinjoji daga Gombe zuwa Kano.
Hadarin ya faru ne, inda wata mota mai lambar rajista KTG 181 ZZ da ke dauke da fasinjoji 19 ta afka cikin hadari.
Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin.
Kwamandan Sector, CC Apaji Danladi Boyi, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai.
A cewar sa, binciken farko ya nuna cewa gudu fiye da kima, gajiya da kuma rashin iya sarrafa mota na iya haifar da hadarin, duk da cewa bincike na ci gaba da gudana.
Jami’an FRSC sun kai dauki cikin gaggawa, inda suka ceto wadanda suka jikkata kuma suka garzaya da su zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya, dake Azare, domin kula da lafiyarsu.
An ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na asibitin, inda ake jiran ‘yan uwansu su zo su gane su.
Kwamanda Boyi ya kara da cewa Aikin Operation Zero na ci gaba da gudana a fadin jihar, kuma jami’an hukumar na sintiri sosai a manyan tituna.


