Gwamnatin Jihar Bauchi ta musanta ikirarin da ake yi na cewa Gwamna Bala Mohammed na shirin barin Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa Jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP).
A cikin wata sanarwa da Mai Bawa Gwamnan Shawara Kan Harkokin Yada Labarai, Mukhtar Gidado, ranar laraba ya bayyana cewa wannan ikirarin babu tushe kwata-kwata, inda ya jaddada cewa Gwamna Mohammed bai taba tunanin barin PDP ko yanke wani mataki na shiga PRP ba.
“Mun lura da wani bayanin da aka danganta da Sakatare na Yada Labarai na PRP na Jihar Bauchi, wanda ke ikirarin cewa ba a maraba da Gwamna Bala Mohammed a cikin jam’iyyar,” in ji Gidado.
“Wannan ikirarin bashi da tushe kuma za a iya watsi da shi a matsayin magana wanda ke neman daukar hankali amma shiru a fuskar ƙarya zai iya fassaruwa a matsayin amincewa, shi ya sa muka ga dacewar fitar da wannan bayani,” ya kara da cewa.
Sanarwar ta bayyana cewa ikirarin da aka danganta da jami’in PRP din ba gaskiya ba ne, kuma kirkiraren rubutu ne kawai.


