Dalilan da su ka sanya sauya shekar Gwamna Abba zuwa APC ya samu tsaiko.
An gano dalilan da suka sa aka dage sauyin sheƙar Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, zuwa jam’iyya mai mulki ta APC, bayan an riga an kammala shirye-shirye na farko.
A ranar Juma’a, wasu majiyoyi sun rawaito cewa gwamnan ya kammala shirye-shiryen sanar da sauyin jam’iyyarsa zuwa APC a ranar Litinin.
Kafin a dage batun sauyin jam’iyyar, hedikwatar jam’iyyar APC ta ƙasa ta shirya cewa gwamnan zai zama mutum na farko da za a yi wa rajista a Kano a sabon tsarin rajistar yanar gizo na jam’iyyar.
Bisa tsarin da aka fara tsara wa, tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ne zai raka gwamnan zuwa mazabarsa ta Diso domin yin rajista a shafin yanar gizon jam’iyyar tare da karɓar katin jam’iyya.
Bayan kammala rajistar gwamnan, an shirya cewa nan take zai raka Ganduje zuwa garinsa na asali a karamar hukumar Dawakin Tofa domin sabunta rajistarsa a sabon shafin yanar gizon jam’iyyar.
Sai dai wasu majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya bayar da umarnin a dakatar da sauyin shekar ta Abba har sai an yi ƙoƙari wajen shawo kan uban gidansa na siyasa, Rabiu Kwankwaso.
A cewar majiyoyin, shirin Kwankwaso na sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC ya sauya lissafin APC.
“Fadar Shugaban Ƙasa na da bayanan sirri cewa Kwankwaso ya gana da Obasanjo da Peter Obi, kuma akwai yiyuwar su haɗa kai domin kalubalantar Tinubu a 2027 kuma Tikitin Obi/Kwankwaso haɗin gwiwa ne mai ƙarfi da zai iya sauya ma’aunin siyasar APC.
“Kuma idan babu Kwankwaso, ƙarfin siyasar gwamnan zai ragu, saboda haka Tinubu na sake tunani kan sauyin jam’iyyar Gwamna Yusuf.
Sai dai wasu majiyoyi sun shaida wa wannan jarida cewa gwamnan da kansa ne ya nemi ƙarin lokaci domin ya samu damar shawo kan ƙarin mambobin Majalisar Dokoki ta Jiha da ta Ƙasa su bi sahunsa wajen sauyin jam’iyyar.
Wasu majiyoyi da ba a tabbatar da su ba sun kuma shaida cewa matsin lambar da gwamnan ke fuskanta ta sanya shi cikin ruɗani, har ta kai ga yana tunanin janye batun sauyin jam’iyyar tare da komawa ya sake haɗewa da uban gidansa Kwankwaso.


