Gwamnatin jihar Gombe ta raba jimillar Naira miliyan 14 ga iyalan ’yan jarida bakwai da suka rasu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a kan hanyar Billiri–Kumo.

Hatsarin ya auku ne a ranar Litinin, 29 ga Disamba, 2025, yayin da ’yan jaridan ke dawowa daga bikin auren wani abokin aikinsu da aka gudanar a Karamar Hukumar Kaltungo.
Kowane iyali daga cikin iyalan da abin ya shafa ya karɓi Naira miliyan 2 daga Gwamnatin Jihar Gombe a matsayin tallafin kuɗi domin taimakawa wajen ɗaukar nauyin jana’iza da sauran buƙatu masu muhimmanci.
Wannan tallafi na daga cikin ƙudurin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na rage raɗaɗin wannan babban rashi da ya faɗa wa iyalan da abin ya shafa.
Da yake jagorantar rabon tallafin a madadin Gwamnan, Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya bayyana cewa tun farko an riga an bai wa iyalan waɗanda suka jikkata wani tallafi na gaggawa nan take bayan aukuwar lamarin.
Ya ƙara da cewa Gwamnan ya ɗauki dukkan nauyin jinya da kuɗaɗen asibiti na waɗanda suka samu raunuka kuma a halin yanzu suke karɓar kulawa a asibiti.
Farfesa Njodi ya jaddada ƙudurin gwamnatin yanzu wajen kula da walwalar ’yan jarida, tare da nuna alhini mai zurfi kan wannan babban rashi da ya shafi Jihar Gombe da kuma aikin jarida gaba ɗaya.

“Zuciyoyinmu sun kasance cikin baƙin ciki tun bayan wannan mummunan lamari, duk da cewa ba za mu iya dawo da waɗanda suka rasu ba ko mu biya diyya daidai da girman asarar, Mai Girma Gwamna ya amince da wannan tallafi domin taimakawa wajen jana’iza, tare da ɗaukar nauyin jinyar waɗanda suka tsira,” in ji shi.
Ya jaddada cewa kuɗaɗen ba diyya ba ne, illa alamar tausayi da jinƙai, domin tallafa wa iyalan a wannan mawuyacin lokaci.
Farfesa Njodi ya kuma isar da ta’aziyyar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ga iyalan mamatan, Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), shugabanci da ma’aikatan Hukumar Talabijin ta Ƙasa (NTA Gombe), da kuma daukacin al’ummar kafafen yaɗa labarai, inda ya roƙi iyalan da abin ya shafa su karɓi lamarin a matsayin ƙaddarar Allah.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), Kwamared Alhassan Yahya Abdullahi, ya bayyana matuƙar godiya ga Gwamnatin jihar Gombe bisa abin da ya kira da tausayi da kuma tallafi na musamman da ba a taɓa ganin irinsa ba.
Ya ce ’yan Kungiyar NUJ a faɗin ƙasar nan suna matuƙar jin daɗin tallafin da aka bai wa iyalan mamatan da kuma ’yan jaridan da ke karɓar jinya a halin yanzu.
Kwamared Alhassan Yahaya ya kuma yi kira gwamnatin tarayya da ta hanzarta aiwatar da tsarin inshorar rayuwa da lafiya ga ’yan jarida, tare da roƙon gwamnatocin jihohi, ciki har da Gombe, su shiga cikin shirin da zarar an fara aiwatar da shi.
Babban Manajan NTA Gombe, Abubakar Adamu, ya bayyana godiyar Daraktan-Janar na NTA, Salihu Dembos, ga Gwamna Inuwa Yahaya bisa karamci da tausayi da ya nuna, inda ya ce daukacin iyalan NTA a faɗin ƙasar nan na girmama Gwamnatin jihar Gombe ƙwarai da gaske bisa wannan gagarumin tallafi.
Da yake magana a madadin iyalan mamatan, Barrista Abubakar Ahmed, ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya kan wannan tallafi, yana mai bayyana shi a matsayin na farko irinsa a tarihin jihar Gombe.

“Wannan tallafi na Naira miliyan 2 ga kowane iyali zai taimaka matuƙa wajen biyan buƙatun gaggawa da na dogon lokaci na iyalan da aka bari, sannan haƙiƙa mun rasa kalmomin godiya, Allah Ya saka wa Gwamna da gwamnatinsa da alheri mai yawa,” in ji shi.

