Gwamnatin kasar Guinea ta soke jam’iyyun siyasa 40 a kasar, inda ta ce a wata doka da ta wanzar ranar Jumu’a za’a rufe duk manya da kananan ofisoshin jam’iyyun 40 a fadin kasar, kuma za’a haramta musu amfani da duk wata alama ko zane dake nuni jam’iyyar.
Dokar ta ce jam’iyyun sun kasa sauke hakkin doka, kamar aikewa da bayanan kudaden su. Da yawa daga cikin jam’iyyun sun koka da wannan hukunci, inda suka dage akan sun yi duk wani abu da doka ta tanada.
Babban dan jam’iyyar adawa a kasar ya ce turjiya kai tsaye ga shugaban kasar mai ci a yanzu ita ce kadai hanyar da za’a kawo sauyi.
Shugaba Mamady Doumbouya, wanda da soja ne, yayi juyin mulki a shekarar 2021, daga baya kuma ya ci zabe na zama shugaban kasa har zuwa shekaru 7 a watan Disamba, wanda sauran ‘yan takara suka kalubalanta. Ana sa ran yin zaben ‘yan majalisar dokokin kasar a watan Mayu.


