Gwamnatin tarayyar Najeriya da ta jihar Kano da kuma gidauniyar rukunin kamfanonin Dangote, sun cimma yarjejeniyar haɓakawa, tare da kula da babbar cibiyar koyon sana’o’i ta Dangote (Dangote Ultramodern Skills Acquisition Center) da ke birnin Kano.
Wannan mataki dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Hukumar Ilimin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (STSB), Farfesa Dahiru Sale Mohammed, ya fitar a madadin Kwamishinan Ilimi na jihar.
A karkashin wannan sabuwar dangantaka, ɓangarorin uku za su dauki nauyin garambawul da inganta kayan aikin cibiyar, sannan su tabbatar da dorewar ayyukanta na tsawon shekaru 20 masu zuwa.
Cibiyar, wacce aka gina domin bai wa matasa horo kan kwarewar hannu da fasahar zamani, ana sa ran za ta kasance kashin baya wajen rage radadin rashin aikin yi a jihar ta Kano da ma makwabtanta.
Farfesa Dahiru Sale ya bayyana cewa wannan yunkuri zai tabbatar da cewa cibiyar ba ta durkushe ba kamar yadda wasu ayyukan ke yi idan aka samu canjin gwamnati, duba da tsarin kula da ita na dogon lokaci da aka kulla.
Jihar Kano dai ita ce jiha mafi yawan jama’a a arewacin Najeriya, inda matasa ke da kaso mafi tsoka. Wannan cibiya za ta mayar da hankali ne wajen koyar da sana’o’in da suka dace da bukatun karni na 21, domin ba wa matasa damar dogaro da kansu maimakon jiran aikin gwamnati.
Sanarwar ta jaddada cewa an kammala dukkan shirye-shiryen fara aikin fito da sabuwar fuskar cibiyar nan ba da jimawa ba.


