Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Wata Mace Ta Mutu A Hannun ‘Yan-Fashin Daji, Wata Ta Haihu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya Ta Mika Koke Ga FIFA Tana Zargin DR Congo Ta Sanya ‘Yan Wasan Da Basu Cancantaba Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Tawayen M23 Masu Samun Goyon Bayan Rwanda Basu Jamye A Ulvira Ba Labarai
  • Afirka Ta Kudu Ta Kama ‘Yan ƙasar Kenya Su Bakwai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Sun Kama Akalla Mutane 13 A Wani Coci A Jihar Kogi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamnatin Najeriya Ta Dauki Matakai Don Farfaɗo Da Maɗaba’ar Gwamnati
Published: December 18, 2025 at 10:56 PM | By: Bala Hassan | Updated: December 19, 2025

Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakai don farfaɗo da Maɗaba’ar Gwamnati da aka yi watsi da ita, bayan shekaru ana tafka asara.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya za ta ɗauki tsauraran matakai domin kawo ƙarshen shekaru na asara da sakaci bayan Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’umah, Alhaji Mohammed Idris, ya kai ziyarar duba Maɗaba’ar Gwamnati da aka daɗe da yin watsi da ita a Abuja, a ranar Alhamis.

A yayin ziyarar, Ministan ya bayyana matuƙar damuwa game da halin da wurin yake ciki.

Ya bayyana cewa watsi da kamfanin ya jawo asarar biliyoyin naira, wanda abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma ya saɓa wa salon Gwamnatin Tarayya da ta tanada, ɗaukar mataki da kuma amfani da dukiyoyin jama’a yadda ya dace, a ƙarƙashin Manufar “Renewed Hope” ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ministan ya tuna cewa an aza tubalin ginin cibiyar tun a shekarar 2001 a zamanin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo, inda ya bayyana cewa aikin ya kai kusan kashi 70 cikin 100 na kammalawa, tare da samar da manyan na’urorin ɗab’i tun a shekarar 2007. Abin mamaki kuma, yawancin injinan da aka shigo da su daga ƙasashe irin su Jamus da Indiya har yanzu ba a buɗe su daga akwatunan su na asali ba fiye da shekara goma, inda wasu daga cikin fasahohin su ma suka zama tsofaffi sakamakon dogon sakaci.

Ya ce: “Abu ne mai taɓa zuciya ganin irin wannan asara a tsakiyar Abuja,” inji Ministan, yana mai cewa, “A daidai lokacin da gwamnati take ƙoƙarin tanadin albarkatu da dogaro da kai, abin ba zai yiwu ba a bar irin wannan babban jari ya lalace shekara da shekaru.”

Maɗaba’ar Gwamnati, wadda ke aikin bugun takardun Gwamnatin Tarayya, ita ce ke da alhakin gurza muhimman takardun ƙasa, ciki har da Jaridar Gwamnatin Tarayya (Federal Government Gazette) da sauran muhimman wallafe-wallafen Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai.

Ministan ya ce tsawon lokacin da maɗaba’ar ta tsaya ba tare da aiki ba ya tilasta gwamnati ta riƙa fitar da ayyukan ɗab’i zuwa waje, alhali ya kamata a yi su a cikin gida, lamarin da ke rage inganci da ƙarfin ƙasa.

Binciken ya kuma nuna cewa muhimman kayayyakin more rayuwa a wurin, ciki har da sabon janareta mai ƙarfin 2000 KVA da aka girka tun a shekarar 2011, bai taɓa aiki ba, wanda ke nuna yadda aka bar dukiyoyin jama’a ba a amfani da su.

Ministan ya samu rakiyar Babban Sakatare na Dindindin, Daraktan Riƙo da ke kula da sashen, da sauran manyan jami’an ma’aikatar.

Ministan ya bayyana cewa sun yi ziyarar ne domin shugabanni su ga halin da ake ciki da idon su, su yi cikakken nazari, sannan su yanke sahihan shawarwarin gudanarwa.

Ya ce: “Mun zo ne domin mu gani da idon mu. za mu koma mu gabatar da shawarwari masu ma’ana ga ga Shugaban Ƙasa da majalisar zartarwa ta tarayya kan mafi kyawun hanyoyin farfaɗo da wannan Maɗaba’ar Gwamnati tare da amfani da ita domin amfanin ‘yan Nijeriya.”

Ministan ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta ci gaba da yin shiru kan lalacewar dukiyoyin ƙasa ba, inda ya tabbatar da cewa za a ɗauki matakai masu ƙarfi domin dawo da darajar jarin da aka riga aka zuba da kuma hana ƙarin asara.

Ya kuma sake jaddada ƙudirin ma’aikatar yaɗa labarai da wayar da kai na gaskiya, kyakkyawan shugabanci da ingantaccen sarrafa albarkatun jama’a, bisa ga umurnin Shugaba Tinubu na cewa duk nairar da aka kashe dole ne ta haifar da wani amfani ga ‘yan Najeriya.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Boko Haram Sun Dauke Kansiloli A Borno
Next Post: Fintiri: Zamu Maida Jihar Adamawa Sabuwar Duniya

Karin Labarai Masu Alaka

Kanal Sani: Idan ‘Yan-Ta’adda Zasu Mutunta Sulhu To Gwamnati Ta Duba Hakan Labarai
Zelensky Na Ukraine Zai Gana Da Takwaransa Na Faransa A Yau Labarai
An Samar Da Dala Kusan Biliyan Biyu Don Yakar Polio Labarai
Trump Da Bin Salman Da Wasu Kasashe Za Su Sa Hannu A Rikicin Sudan Labarai
Gwamnan Jihar Gombe Ya Umurci A Rufe Makarantu Labarai
Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Lumbala Shekaru 30 Bisa Laifin Cin Zarafi Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Kamfanin Hakar Ma’adanai Na Kasar Kanada Ya Cigaban Da Aikinsa
  • Za’a Koyawa Yara Tarihin Shugaba Donald Trump Saboda Rayuwarsa Akwai Darasi Wajen Jajircewa Da Kwazo
  • Rahoton MDD Yace An Kashe Fiye Da Farar 1000 A Sudan
  • Wata Mace Ta Mutu A Hannun ‘Yan-Fashin Daji, Wata Ta Haihu
  • Shugaba Tinubu Ya Gargadi Gwamnoni Game Da Rike Kudaden Kananan Hukumomi Tare Kuma Da Bada Tabbacin Kafa ‘Yan Sandan Jihohi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Jirgin Sojin Saman Najeriya Yayi Hatsari a Jihar Neja Labarai
  • Samar Da Tsaro A Jihar Kano Ba Sai An Sa Siyasa Ba! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ana Gudanar Da Zanga-Zangar Adawa Da Gwamnati A Kasar Tunisiya Siyasa
  • Rwanda Tana Keta Yarjejeniyar Zaman Lafiya – Tshisekedi Labarai
  • Ga Dukkan Alamu Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Bai Kare Ba Sauran Duniya
  • Alhassan Yayi Nasarar Kifar Da Wurkilili A Gasar Damben Gargajiya Wasanni
  • Rundunan  ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Ta Miƙa Miyagun Ƙwayoyi Da Ta Kama Wa NDLEA. Labarai
  • ECOWAS Zata Taimakawa Kasar Benin Da Dakarun Soji Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.