Hukumar NDLEA dake ayyukan hana sha da fataucin miyagun kwayoyi da ababen sanya maye a Najeriya tace tana tsananta bincike akan ‘yan matan nan guda biyu da ak damke yayin da sukayi yunkurin kai kwayar Tramadol ga wasu mutane dake tsare a gidan gyaran hali a Kano.
Jami’an hukumar kula da gidan gyaran halin ne suka damke ‘yan matan Maryam Ali ‘yar shekaru 19 da Hauwa Musa mai shekaru 20 a yayin binciken masu ziyarar daurarru a gidan gyaran hali na Goron Dutse a Kano.
Maryam Ali da Hauwa Musa sun boye kwayoyin tramadol din ne a cikin gurasa da sauran kayayyakin cimaka da suka dauko domin kaiwa samarin su dake daure.
DSP, Misbahu Lawan, kakakin hukumar kula da gyaran hali ta Najeriya shiyyar Kano yace damke ‘yan matan na daga cikin samakon tsauraran matakan da suke dauka akan masu ziyarar daurarru.
Yanzu haka dai hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ta karbi ragamar gudanar da binciken kwakwaf akan wadannan ‘yan mata Maryam Ali da Hauwa Musa.
ASP, Sadiq Muhammad Maigatari, dake zaman kakakin hukumar ta NDLEA a Kano, yace Maryam Ali, guda cikin ‘yan Matan ta shaida musu cewa, tana shirin kaiwa saurayin ta kwayoyin tramadol da aka kamata dasu ne, wanda ke daure a can gidan gyran hali na Goron Dutse a Kano. Tace ita-ma tana amfani da nau’ikan kayayyakin san maye, irin su Codeine da tabar Wiwi.
Wannan yunkurin ‘yan mata domin safarar kwayoyi zuwa cikin gidajen da ake tsare da masu laifi, na kara fito da jan aikin dake gaban gwamnati da hukumominta wajen yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi da ababen sanya maye a Najeriya.


