Isra’ila ta kai wani sabon hari a Tehran da yammacin ranar Lahadi, kuma Iran ta mayar da martani da karin makamai masu linzami, kwana guda bayan kisan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ali Khamenei, wanda hakan ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya da tattalin arzikin duniya cikin rashin tabbas.
Hare-haren na Amurka da Isra’ila da kuma martanin Iran ya haifar da girgizar kasa ta bangarori daban daban daga jigilar kayayyaki zuwa jiragen sama zuwa mai, a daidai lokacin da ake gargadin hauhawar farashin makamashi da kawo cikas ga harkokin kasuwanci a Tekun Fasha, wata babbar hanyar ruwa da kuma cibiyar kasuwancin duniya.
Shugaban Amurka Donald Trump yace an kai harin ne domin tabbatar da cewa Iran ba za ta iya mallakar makamin nukiliya ba, don dakile shirinta na makami mai linzami da kuma kawar da barazana ga Amurka da kawayenta.


