Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe Afrika
  • Hukumomin Bada Agaji Sun Fadakar Da Al’ummar Jihar Gombe Afrika
  • Ana Cigaba Da Shirye-Shiryen Fara Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Zata Samar Da Sabbin Dakunan Karatun Dalibai Afrika
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cire Sharadin Rubuta UTME Ga Masu Neman Shiga Kwalejojin Ilimi Afrika

Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Zata Karbi ‘Yan Gudun Hijirar Da Amurka Ta kora
Published: April 6, 2026 at 7:32 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta sanar cewa za ta karɓi ‘yan ƙasashen waje da Amurka ke korar su daga ƙasar, ƙarƙashin wata sabuwar yarjejeniya da gwamnatin Donald Trump, kamar yadda gwamnati a Kinshasa ta bayyana a cikin wata sanarwa jiya Lahadi.

Gwamnatin ta ce za ta fara karɓar waɗanda aka kora daga watan Afrilu, amma ba ta bayyana adadin mutanen da ta amince za ta karɓa ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa Amurka ce za ta ɗauki nauyin wannan shiri gaba ɗaya, ba tare da wani kuɗi daga gwamnatin Kongo ba. Haka kuma, an tanadi wuraren zama kusa da babban birnin ƙasar, wato Kinshasa, domin sauƙaƙa wa waɗanda za a kawo masauki.

Amurka ta riga ta tura wasu ‘yan ƙasashen waje da aka kora zuwa wasu ƙasashen Afirka da suka haɗa da Ghana, Cameroon, Equatorial Guinea da Eswatini, lamarin da ya janyo suka daga masana harkokin doka da kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam.

Wannan yarjejeniya na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Trump ke ƙoƙarin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Kongo da Rwanda, tare da wata yarjejeniya da ke tabbatar da samun damar Amurka ga muhimman ma’adanan Kongo.

Afrika, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Rundunar Sojin Najeriya Ta Kubutar Da Wasu Mutane 31 Da Aka Yi Garkuwa Dasu
Next Post: Shugaba Trump Ya Kara Matsin Lamba Kan Iran

Karin Labarai Masu Alaka

Kurdawa Sun Gargadi ‘Yan Uwansu Game Da Alaka Da Amurka Wajen Yakar Iran Afrika
‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Cin Karensu Babu Babbaka A Najeriya Afrika
Amurka Zata Kara Tura Sojoji Gabas Ta Tsakiya Afrika
An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano Labarai
China Ta Dawo Da Harajin Magungunan Hana Haihuwa Labarai
Wani Dan Bindiga Ya Harbi Dakarun Tsaron Cikin Gida Su Biyu A Washington DC Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe
  • Hukumomin Bada Agaji Sun Fadakar Da Al’ummar Jihar Gombe
  • Ana Cigaba Da Shirye-Shiryen Fara Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Zata Samar Da Sabbin Dakunan Karatun Dalibai
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cire Sharadin Rubuta UTME Ga Masu Neman Shiga Kwalejojin Ilimi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Alkalan Wasannin Kwallon Kafa A Ghana Zasu Samu Inshora Wasanni
  • FIFA Ta Yi Wa Malaysia Kaca-kaca Wasanni
  • Kasar Amurka Takara Saka Takunkumi Akan Kasar Venezuela Amurka
  • Wani Jirgin Sama Ya Karya Dokar Hana Zirga Zirga Amurka
  • Amurka Zata Aika Jiragen Yaki Biyu Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano Labarai
  • Donald Trump Yace Basu Cimma Matsaya Da Benjamin Natanyahu Ba Afrika
  • Shirin Manuniya Kashi Na Daya, Yau Juma’a 11.21.25 Shirye-Shirye
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.