Sashin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da hare-haren da ‘yan tawayen M23 ke kaiwa gabashin Jamhuriyar Demokradiyar Congo, inda ta bukaci Rwanda ta dena marawa ‘yan tawayen baya, kuma ta cire dakarun ta daga wurin, sannan majalisar ta kara wa’adin dakaraun ta masu samar da zaman lafiya a yankin.
mambobin majalisar 15, wanda suka raja’a kan matsaya daya na warware matsalar, sun kuma bukaci dakarun Congo da su dena marawa kungiyoyi kamar su FDRL baya, kuma Demokradiyar Jamhuriyar Congo ta cika kudurin da ta dauka na kwance damarar kungiyar.
‘Yan hutu da suka tsere daga Rwanda bayan sa hannun su a aikata kisan kiyashi a shekarar 1994, da yai sanadin hallaka ‘yan Tutsi kusan miliyan daya da ‘yan hutu masu matsakaicin ra’ayi, ne suka samar da kungiyar ta FDLR, kuma ‘yan tawayen M23 sun ce suna yaki ne don kare ‘yan kabilar tutsi a gabashin Congo.


