Shugabannin Fulani a Jihar Nejan Nigeria sun koka akan yadda suka ce Jami’an Tsaron ‘Yan-banga na cin zarafin Fulanin ba tare da tantance mai laifi ko mara laifi.
Wannan dai yana zuwa ne bayan da aka yi zargin wasu ‘yan bindiga a yankin karamar Hukumar Mashegu sun ci zarafin shugaban kungiyar makiyaya ta Miyatti Allah tare da wasu Fulanin su 13.
Bayanai dai sun nuna cewa ‘yan bangan sun yima wadan nan Fulani daurin goro tare da gana musu azaba da a yanzu haka suna karbar magani a babbar Asibitin Gwamnati dake Kontagora,
Alh. Muhammadu Mabbe, shine shugaban Fulanin na karamar Hukumar Magama da ya shiga hannun wadan nan ‘Yan banga da a yanzu haka yake kwance cikin wani mawuyancin hali, yace ‘yan bangar sun sameshi a kofar gidan Sarkin koso ne a dai dai lokacin da suke kokarin jana’izar wani yaron su da aka kashe.
Shugaban Babban Jami’i a Ma’aikatar Kula da Harkokin Makiyaya ta Jihar Neja Malam Ababakar Kamfanin Bobi yayi karin haske akan irin azabar da aka basu.
Sarkin Fulanin Minna Alhaji Hasan Shiroro, wanda shima a kwanakin baya yace ‘yan bangar sun bindige yaro kuma nan take ya mutu har lahira.
Mun tuntubi shugaban ‘yan bangar na Jihar Neja Nasiru Muhwmmad Manta, yace basu da hannu a ciki, amma kuma zasu gudanar da bincike akan lamarin.
Tini dai masu kare hakkin dan adam suka bayyana damuwa akan wannan lamari Kwamrade Kabiru Idris Jami’i ne a hukumar kare hakkin dan adam ne a Jihar Nejan, inda yace basu yadda da wannan cin zarafin ba.
Suma masana a fannin tsaron da zamantakewa suka nuna bukatar dakatar da irin wannan daukar doka a hannu, don shawo kan matsalolin tsaro da Najeriya ke fama dashi.


