Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Jirgi Marar Matuka Yayi Luguden Wutan A Abu Dhabi
Published: March 2, 2026 at 8:35 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wani jirgi mara matuki da ya tarwatse ya lalata wani katafaren ginin a birnin Abu Dhabi dake kusa da ofishin jakadancin Isra’ila da wasu ofisoshin jakadanci na kasa da kasa da dama, lamarin da ya haddasa kananan raunuka ga wata mata da yaronta, kamar yadda ofishin yada labarai na gwamnatin Abu Dhabi ya sanar da yammacin ranar Lahadi.

tarkacen jirgin mara matuki sun fado a gaban wani ginin Etihad Towers, bayan wata na’ura ta hana makamin fashewa a kasa, in ji ofishin yada labaran.

Bayan da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hare-hare kan Iran a ranar Asabar, Iran ta ce za ta kai hari kan sansanonin Amurka da ke yankin. Amma kuma ta afkawa yankuna da dama na farar hula da na kasuwanci a duk fadin garuruwan yankin Gulf, lamarin da ke kara fadada tasirin rikicin kan muhimman cibiyoyin zirga-zirgar jiragen sama da na kasuwanci a yankin.

Yayin da hare-haren ramuwar gayya ke ci gaba da yaduwa a jiya Lahadin, sun sake yin kaca-kaca a sassan kasashen Larabawa na yankin Gulf, inda aka ji karar fashewar abubuwa masu karfi a Dubai da Doha babban birnin Qatar da kuma Oman a karon farko.

Sanarwar da ofishin yada labaran gwamnatin Dubai data fitar ta ce, a birnin Dubai, wasu mutane biyu sun jikkata bayan da wasu tarkacen jiragen sama marasa matuka suka fado kan gidaje biyu lokacin da aka kama su.

Afrika, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
Next Post: Isra’ila Takai Sabon Hari Tehran Ranar Lahadi

Karin Labarai Masu Alaka

Malaman Addinin Musulunci Da Kirista Sunyi Bikin Cika Shekara 15 Na Iftar A Najeriya Afrika
Ansamu Girgizar Kasa A Kasar Taiwan Labarai
Kanal Sani: Idan ‘Yan-Ta’adda Zasu Mutunta Sulhu To Gwamnati Ta Duba Hakan Labarai
Zaman Lafiya Yafara Dawowa A Sudan Afrika
Magoya Bayan Dan Hamayya A Afirka Ta Kudu Sun Hallara A Kotu Afrika
Kungiyar Maharba Da ‘Yan Sintiri Sun Samu Kyautar Motoci Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Shugaban Amurka Yace Sojojin Amurka Dana Iran Sunyi Taho Mugama
  • Zanga-Zangar Adawa Da Harin Amurka Da Isra’ila Ya Zamo Tarzoma A Pakistani
  • Isra’ila Takai Sabon Hari Tehran Ranar Lahadi
  • Jirgi Marar Matuka Yayi Luguden Wutan A Abu Dhabi
  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • An Kubutar Da ‘Yan Matan Sakandire Su 24 Na Jihar Kebbi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Ziyarci IBB Siyasa
  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini Afrika
  • An Kashe Mutane 7 A Unguwar Dorayi Dake Kano Najeriya
  • Alaka Na Cigaba Da Kamari Tsakanin Rwanda Da Barundi Labarai
  • Sojojin Amurka Sun Kashe Wasu Fararen Hula Ba Dalili Amurka
  • Gwamna Abba Gida-Gida Na Dari-Darin Shiga APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Emmanuel Macron: Yakamata Wani Sashi Ya Rika Takawa Wani Sashi Birki A Tsarin Demokradiya Amurka Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.