Wani kamfanin hada-hadar kudin Bitcoin a Korea ta kudu, ranar asabar ya bada sanarwar cewa yayi kuskuren turawa Wadanda suke mu’amala da kamfanin fiye da dala bilyan 40 na Bitcoin a zaman tukuici, wanda ya haddasa gonjon Hannayen jarin kamfanin.
Kamfanin mai suna Bithum ya bada baki da neman a masa afuwa, lamarin wanda ya auku ranar Jumma’a tuni kamfanin yace ya maido da kashi 99.7 cikin dari da illahirin kudaden na Bitcoin da ya rarrabar, wanda darajar su ya kai dalar Amurka bilyan 44 a farashinsa na yanzu. Kamfanin ya takaita hada-hada, da suka hada da daukar kudi ga masu mu’amala da kamfanin su 695 cikin minti 35 da yin wannan kuskure.
Da kamfanin yaso ya rabawa masu mu’amala tukuici 2,000 kudin korea ta kudu, kimanin dala daya da centi 40 na Amurka ga ko wani mutum, maimakon haka masu mu’amala da Bithum suka sami kudin Bitcoin 2,000 ga ko wani mutum kamar yadda kafofin yada labarai suka fada.


