Kamfanonin jiragen sama masu jigilar fasinja suna fama da karin farashin mai, yayinda yakin hadin gwiwar Amurka da Isra’ila kan Iran, ya haddasa karancin mai, lamari da ya janyo wa masu balaguro karin kudin tafiye-tafiye, su kuma kamfanonin suke fama da hauhawar farashin mai saboda karancinsa.
Nahiyar Afirka ce tafi fuskantar matsalar ta fuska biyu na karancin mai da kuma karin farashinsa. Kimanin kashi 70 cikin dari na mai jiragen sama suke amfani dashi da kananzur ta mashigin Ruwan Hormuz ake jigilarsu zuwa Afirka, kamar yadda alkaluman kamfanin kididdiga S&P suka nuna.
Kuma tun fara wannan yaki a karshen watan Febawairu, jigilar mai daga matatun mai dake gabas ta tsakiya kusan ya tsaya chick, wadda ya cire kashi daya cikin biyar na mai da duniya take amfani dashi.


