Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Kasar Aljeriya Ta Soke Yarjejeniyar Jirgin Sama Tsakaninta Da Daular Larabawa
Published: February 8, 2026 at 9:31 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Aljeriya ta fara soke yarjejeniyar zirga zirgar jirgin sama tsakaninta da hadaddiyar daular larabawa, wacce kasashen suka rantabawa hanu cikin watan mayun shekara ta 2013, kamar yadda aka ji daga kafofin yada labaran kasar a ranar Asabar.

Ba’a bada bayani kan dalilin nan da nan kan daukar wanan mataki ba, amma kafofin yada labaran kasar na matukar sukar hadaddiyar daular larabawan a cikin watannin baya bayan nan kan zargin kasar tana neman haddasa husuma a yankin.

A cikin sanarwar da gidan rediyon kasar ya bayar, yace, “Aljeriya ta fara daukar matakan kawo karshen yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla game da zirga zirgar jirgin sama tsakanin kasashen biyu, da aka yi cikin watan mayun shekara ta 2013, daga bisani aka karfafa shi tare da dokar shugaban kasa cikin watan Disamba 2014.”

Hadaddiyar daular larabawan dai bata furta komi ba game da wannan sanarwa.

A cikin watan oktoban bara, shugaban kasar Aljeriya Abdelmajid Tebboune yace aljeriya tana da kyakkyawar dangantaka da kasashe dake yankin Gulf, in banda kasa daya, a zaman gugar zana ga hadddiyar daular larabawa.

Ya zargi kasar da bai bayyan sunanta ba, da yin shishshigi cikin harkokin cikin gidanta da nufin sukurkuta harkokin kasar.

Labarai, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Muhawara Mai Zafi Tsakanin APC da ADC
Next Post: Iran Tace Farisa Zata Kai Hari Kan Mayakan Amurka

Karin Labarai Masu Alaka

Gidauniya: An Fara Tiyatar ‘Hernia’ Da ‘Hydrocele’ Kyauta A Jihar Katsina Labarai
Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar Amurka
An Kashe Mutane 25 Yayin Kai Wasu Hare Hare Jihar Adamawa Labarai
An Gudanar Da Zanga-Zanga A Kasar Somaliya Labarai
Mayakan M23 Sun Tsagaita Wuta A Gabashin Kwango Labarai
Kasar Masar Ta Dakatar Da Wasu Ayyukan Da Ake Amfani Da Man Fetur Da Diesel Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sarkin Musulmi Ya Ziyarci Shugaba Bola Tinubu Afrika
  • Bankin Duniya Zaibawa Kasar Mozambique Lamunin Dala Bilyan Shida Labarai
  • MDD: Fiye Da Farar Hula Metan 200 Suka Mutu A Sudan Afrika
  • Hukumar Hakar Ma’adanai A Kasar Zambiya Ta Dakatar Da Ayyukanta Kimiya
  • An Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Game Da Matsalar Tsaro A Najeriya Najeriya
  • Majalisar Dattawar Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet Labarai
  • Dottin Shara Ya Damu Jama’ar Havana Kasar Cuba Labarai
  • ‘Yan Tawayen Kasar Kwango Ne Suka Kai Hari Filin Jirgin Saman Kisangani Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.