Ranar Litinin, Rasha ta zargi ukraine da kai hari kan gidan shugaban Rasha Vladimir Putin, daga nan tayi alkwarin zata dauki fansa duk da cewa bata nuna wata shaidar harin ba, tuni dai Ukraine tayi watsi da zargin, tana mai cewa Rasha tana kokarin tayi kafar ungulu akan shawarwarin neman kawo karshen yaki da kasashen biyu suke yi.
Musayar zazzafar kalamai tsakanin makwabtan kasashen biyu ranar litinin, ciki harda ikirarin da Rasha tayi cewa harin yasa zata sake nazarin matsayar ta a shawarwarin neman kawo karshen yakin, wadda hakan zai maida hanun agogo baya a yunkurin wanzar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Donad Trump na Amurka yace Putin ya gaya masa batun harin, da suka yi magana ta wayar tarho ranar litinin da safe, yace labarin ya bakanta masa rai, duk da haka yace har yanzu yana ganin an kusa a cimma matsayar da zata wanzar da zaman lafiya a rikici tsakanin kasashen biyu.
Da aka tambaye shi ko hukumomin leken asirin Amurka suna da shaidar zargin harin da Putin yayi, shugaba Trump, yace ‘Zamu mu bincika mu gani.”


