Kasashen Faransa da Italiya, sun nuna rashin amincewar su da matakan soji da Amurka da Isra’ila suka dauka, kamar yadda majiyoyi suka fada jiya talata, yayinda shugaban Amurka Donald Trump, ya soki kawayen Amurka dake kungiyar tsaro ta NATO a turai cewa basu taimaka ba a yakin da suka kaddamar a gabas ta tsakiya na tsawon wata daya, wadda yake nuna rarrabuwar kawuna tsakanin membobin kungiyar.
Shugaba Trump ya zargi Faransa da hana jirgin sama dauke da kayan yaki zuwa Isra’ila bi ta sararin samaniyarta, a wani bayani da ya wallafa a dandalin sada zumunta na kansa da ake kira Truth Social, Trump ya rubuta cikin manyan haruffa cewa Faransa taki ta taimaka.
Fadar shugaban Faransa tace tayi mamakin furucin na shugaban Amurka, tace manufofi da matsayar Faransa kaifi daya ne tun lokacin da aka fara wannan yaki.
Wani jami’in difilomasiyya, da wasu majiyoyi biyu da suke da masaniya dangane da batun sun fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, matakin na Faransa wanda ya faru a karshen makon da ya gabata, shine irinsa na farko da Faransa ta dauka tun fara wannan yakin ranar 28 ga watan Febwairu.
Majiyoyin sukace Isra’ila ta so tayi amfani da sararin samaniyar Faransa tayi jigilar makamai domin yakin Iran.


