Wata kotu a kasar Faransa ta yanke hukun
cin daurin shekaru 30 a gidan kurkuku a kan tsohon madugun ‘yan tawayen Kwango ta Kinshasa, Roger Lumbala, wanda ta samu da laifuffukan cin zarafin bil Adama a lokacin yakin Kwango na biyu.
‘Yan rajin ganin an hukumta masu aikata irin wadannan laifuffuka a gadin duniya sun yaba da wannan hukunci a zaman babban ci gaba na hukumta masu hannu a wannan yakin da ya kashe miliyoyin mutane.
A lokacin da yake bayyana hukuncin, alkalin wannan kotu dake birnin Paris, Marc Sommerer, yace Lumbala ya aikata ko ya bada umurnin aikatawa, ko ya tallafa wajen aikata munanan laifuffuka da kashe-kashe da fyade, da gana azaba, da bautarwa da sata da wawusa ko lalata dukiyoyi.
Wadannan laifuffukan da aka tuhumi Lumbala da aikatawa suna da alaka da wani farmakin da wata kungiyarsa mai samun goyon bayan kasar uganda a lokacin, ta kai a shekarun 2002 da kuma 2003 a arewa maso gabashin Kwango.
Sun kai hare-haren ne a kan ‘yan kabilun Nande da Bambuti wadanda suka zarga da laifin goyon bayan wata kungiyar daban ta sojojin sa kai a yankin.
An gudanar da yakin Kwango na biyu daga shekarar 1998 zuwa 2003. Kasashe har guda 9 suka tsoma baki da hannu a wannan yaki, kuma an kashe mutane fiye da miliyan 5, cikinsu har da wadanda suka mutu a sanadin yunwa da kuma cututtuka.


