Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bada belin Kwamishinan Kuɗi na Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, kan kuɗi Naira miliyan 500, tare da sharuɗɗan samun wakilai biyu masu ƙarfi da za su tsaya masa.
Kotun ta ƙayyade cewa waɗanda za su tsaya masa dole ne su kasance da matsayi mai ƙarfi a cikin al’umma kuma su mallaki kadarori a babban birnin tarayya, Abuja.
Wannan mataki ya biyo bayan gurfanar da kwamishinan a gaban kotu bisa zargin aikata laifuka da suka shafi almundahana da kuma bada tallafi ga ayyukan ta’addanci, kamar yadda hukumar EFCC ta bayyana.
Shari’ar za ta ci gaba da gudana yayin da ake jiran cikar dukkan sharuɗɗan belin.


