Tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Najeriya kuma Babban Manajan Kada Warriors, Garba Lawal, ya nuna matuƙar sha’awarsa ga filin wasa na Rashidi Yekini Mainbow George Innih, Ilorin, yana mai bayyana shi a matsayin “matsayin irin na Turai.”
Tsohon ɗan wasan gaba na Super Eagles, wanda ya yi wasanni 57 wa ƙasa, ya yi wannan furucin ne yayin da yake magana da manema labarai a lokacin wasan da ƙungiyar Kada Warriors ta yi da ƙungiyar ABS FC a gasar NNL , mako na shida a Ilorin, inda ƙungiyarsa ta yi nasara da ci 1-0.

Garba Lawal ya yaba wa gwamnatin jihar Kwara saboda saka hannun jari a fannin kayayyakin wasanni masu inganci, yana mai cewa irin waɗannan ci gaba suna da matuƙar muhimmanci ga ci gaban ƙwallon ƙafa a dukkan matakai a Najeriya.
Lawal ya ƙara da yin kira ga me da irin waɗannan gyare-gyare a fannin kayayyakin more rayuwa a jihar Kaduna, yana mai bayyana cewa an riga an fara aikin gyara a filin wasa na ABS da ke Kaduna a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin inganta wurare ga ƙungiyoyi da ‘yan wasa.
A cewar Lawal, filayen wasa masu kyau ba wai kawai suna inganta wasa ba ne, suna rage haɗarin raunuka da kuma taimaka wa ‘yan wasa su bayyana kansu da kyau a filin wasa.


