Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Matar El-Rufai Ta Roƙi Tinubu Ya Tabbatar An Yi Wa Mijinta Adalci
Published: July 8, 2026 at 9:29 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Matar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta yi kira ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya tabbatar an yi wa mijinta, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, adalci yayin da yake fuskantar shari’ar da ake yi masa.

Da take magana a ranar Talata a gidan iyalansu da ke Abuja tare da ɗayar matar El-Rufai, Hajiya Aichatou El-Rufai, Asia ta ce ba sa roƙon Shugaban Ƙasa ya tsoma baki a cikin shari’ar, sai dai su tabbatar an mutunta haƙƙoƙin El-Rufai da kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada.

Ta tuna irin goyon bayan da ita da mijinta suka bai wa Tinubu a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, tana mai cewa sun yi aiki tuƙuru domin samun nasararsa a Jihar Kaduna.

“Mai Girma Shugaban Ƙasa, na yi muku yaƙin neman zaɓe. Na zagaya ko’ina cikin Jihar Kaduna domin neman muku ƙuri’u. Mijina ya tsaya tsayin daka tare da ku. Shin wannan ne sakamakon da iyalinmu suka cancanta?” in ji ta.

Asia ta roƙi Shugaban Ƙasa da ya tabbatar an bai wa El-Rufai damar samun kulawar lafiya, ganawa da lauyoyinsa da kuma iyalansa, tana mai jaddada cewa abin da suke nema shi ne adalci da kuma mutunta doka.

“Ba na roƙon ku ku hana a gurfanar da shi a kotu ba, abin da muke nema shi ne a ba shi haƙƙoƙin ɗan Adam na asali da Kundin Tsarin Mulkin da kuka rantse za ku kare ya tanada,” in ji ta.

Ta kuma yi zargin cewa El-Rufai, wanda ta ce likitoci sun tabbatar yana fama da hawan jini da kuma ciwon sukari, ba ya samun isasshiyar kulawar lafiya yayin da yake tsare.

A cewarta, hana likitansa na kashin kansa, lauyoyinsa da ‘yan uwansa damar ganinsa ya jefa iyalan cikin damuwa matuƙa.

“Mu iyalansa muna cikin firgici. Muna rayuwa cikin fargabar wata rana mu wayi gari da labarin da ba ma fatan ji,” in ji ta.

Asia ta ce ya kamata a bai wa mijinta damar kare kansa yadda ya kamata yayin da shari’arsa ke gudana.

“Ya kamata a ba shi beli cikin sharuddan da suka dace. Idan yana da laifi, kotu ce za ta yanke hukunci. Idan kuma ba shi da laifi, ita ma kotu ce za ta tabbatar da hakan,” ta ƙara da cewa.

Wannan roƙo ya biyo bayan kama likitan El-Rufai, Bello Abubakar, da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka masu Alaƙa (ICPC) ta yi bisa zargin bayar da bayanan da ake zargin ba daidai ba ne game da ziyarar duba lafiyar tsohon gwamnan yayin da yake tsare.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Sarakunan Gombe Da Zazzau Sun Yi Kira Ga ‘Yan Najeriya Su Rungumi Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
Next Post: Gwamnonin Arewa Sun Kaddamar da Kwamitin Asusun Tsaro

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Gudun Hijira A Kasar Libya Suna Fuskantar Cin Zarafi Afrika
Jamhuriyar Congo Zata Cigaba Da Fitar Da Ma’adanai Afrika
Congo Ta Kawo Karshen Cutar Kyandar Birai Afrika
Jam’iyar APC A Jihar Gombe Ta Tsayar Da Jamilu Isiyaku Gwamna Takarar Gwamna Afrika
Nuhu Ribadu Ya Mika Dalibai 100 da Aka Ceto Ga Gwamnatin Jihar Neja Labarai
Yeriman Ingila Ya Gana Da Yeriman Saudiya Mai Jiran Gado Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • KADCCAM Ta Yaba Da Shuka Bishiyoyi A Kaduna Afrika
  • ‘Yan Sanda A Tsibirin Bahamas Sun kama Mijin Wata Ba Amurkiya Amurka
  • Gwamnan Gombe Ya Ƙara Tallafin N148.76bn Domin Aiwatar da Sabon Tsarin Albashi A Jami’ar Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Zuwa Jami’ar Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurkawa Sun Nuna Bacin Rai Saboda Yawaita Kashe ‘Yan Kasar Amurka
  • Mayakan RSF Sun Zafafa Kai Hare Hare Da Jirgi Maras Matuki A Sudan Labarai
  • Yamai Cikin Rashin Tabbas Bayan Karar Harbe-Harbe Da Aka Ji Afrika
  • Ganduje Ya Nisanta Kansa Da Batan Dadiyata Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.