Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Mayakan ISWAP Sun Kai Farmaki Kan Sojojin Najeriya
Published: January 30, 2026 at 5:36 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 30, 2026

Mayakan ISWAP da jiragen yaki marasa matuka wato drones suka rufawa baya, sun kai hari kan wani sansanin sojoji a jihar Barno,suka kashe sojoji masu yawa da asubahin ranar Alhamis, wannan yana kunshe ne cikin bayani da sojojin kasar suka bayar. Kuma wannan shine hari na biyu da mayakan suka kai wa dakarun kasar a yankin cikin makon nan.

Jiragen drones da mayakan ISWAP suke amfani da su a hare haren da suke kaiwa a baya bayan nan ya zafafa tarzoma a yankin, kamar yadda kakakin rundunar sojin Najeriya Leftanar kanar Sani Uba ya fada.

Mayakan na ISWAP sun afkawa sansanin dake Sabon Gari cikin dare sosai, suka kutsa cikin sansanin na wani dan gajeren lokaci, yayin da kuma ake gwabza fada, jiragen yakin su na drones, suka lalata motocin aikin sojojin, manya da kanana.

Wasu majiyoyi biyu ta fuskar tsaro sunce an kashe akalla sojoji 9, da ‘yan banga biyu, wasu 16 kuma suka jikkata.

A bana dai sojojin Najeriya sun kutsa sosai cikin yankin da mayakan sakan suke, a wani sabon yunkuri na kai musu farmaki a inda suke.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Matsalolin Masarautun Kano Sun Kawo Karshe
Next Post: Gwamnatin Sojan Burkina Faso Ta Soke Jam’iyyun Siyasar Kasar

Karin Labarai Masu Alaka

Ganduje: Mun Janye Shirin Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano Najeriya
Mizanin Tattalin Arzikin Najeriya Na 2024 Ya Karu Da Kashi 3.84% Labarai
Wike: Bazamuyi Sake Fubara Ya Sake Samun Nasara Ba Najeriya
Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Kasafin Kuɗin 2026 Najeriya
Za’a Fuskanci Bala’in Yunwa A Najeriya Labarai
Masarautar Borgu a Jihar Neja na neman daukin Gwamnatin Najeriya akan matsalar rashin tsaro Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Indonesia Zata Kafafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Gaza
  • Shugabannin Kasar Australia Sun Bukaci ‘Yan Kasar Suyi Zanga Zanga Cikin Lumana
  • Shugaban Afrika Ta Kudu Yanuna Goyon Bayan Kawo Karshen Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine
  • Ethiopia Tana Horas Da Dakarun RSF A Wani Sansani
  • Majalisar Dottijan Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Na’ura

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Asabar 11.15.2025 Rediyo
  • FIFA, Ta Raba Jaddawalin Rukuni Na Gasar Kofin Duniya 2026. Wasanni
  • Okoye Na Shirin Maye Gurbin Nwabali, AFCON 2025: Wasanni
  • Kama Muhyi Magaji Siyasa ce Kawai Inji Gwamnatin Kano Labarai
  • Jakadan Kasar Sin a Najeriya Ya Ziyarci Tinubu Najeriya
  • Gwamnatin Kasar Benin Ta Nemi ‘Yan Kasa Su Kwantar Da Hankali Afrika
  • Maharan Bindiga Sun Kashe Mutane 12 Masu Hakar Ma’adanai A Jihar Filato Labarai
  • Anakan Bincike Wajen Gano Dan Bindigar Da Ya Kashe Dalibai Biyu A Jihar Rhode Island Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.