Tasirin Lionel Messi da Cristiano Ronaldo: Yasa Farashin Gasar Cin Kofin Duniya ta FIFA 2026, Ya tashi zuwa matsayi mafi girma yayin da wani sabon salo na tallace-tallace ya bude.
Har yanzu a kwai sauran kwanaki fiye da 180, kafin a fara gasar cin Kofin Duniya na 2026, duk da haka tsammanin da ake yi game da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo ya riga ya sanya gasar ya shiga cikin wani sabon babi a tarihance.

Yayin da magoya baya ke tururuwa don samun tikitin shiga gasar da kasashen Amurka, Kanada, da Mexico za su karbi bakuncinta.
Hakan na faruwa ne kasancewar jaruman biyu Lionel Messi na Argentina da kuma Cristiano Ronaldo na Kasar Putugal suna cikin wannan gasa ta duniya -kasan cewar fitattun ‘yan wasan biyu ya haifar da karuwan da ba’a taba yin taba a duniya wacce ke nuna wani sabon salo na zurfafa bincike kan lamarin mai cike da farin ciki.


