‘Yan gwagwarmaya da suka shirya jerin gwanon jiragen ruwa dauke da tallafin abinci da magunguna zuwa Gaza a bara, wadanda Isra’ila ta hana su kai tallafin suna shirin za su sake gwada daukar matakin a bana ma. Suna sa ran jiragen ruwan da zasu shiga tattakin su ninka na bara dauke da ma’aikatan kiwon lafiya fiye da dubu daya.
A bara Isra’ila ta dakatar jerin gwanon jiragen ruwan da suka kai 40 cikin watan oktoban bara, suka kama ‘yar gagwarmayan nan daga Sweeden Greta Thunberg da wasu mutane 450.
‘Yan Gwagwarmaya da suka hallara a harabar gidauniyar marigayi tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela a ranar laraba a birnin Johanesburg, sunce jiragen ruwa 100 ne suke sa ran za su shiga tafiyar ta bana.
Jami’an Isra’ila sun sha yin tur da Allah wadai da matakan na ‘yan gwagwarmaya, suna masu cewa wannan ba komi bane, illa halin dan zakara mai neman suna.
Isra’ila wacce take da iko kan dukkanin hanyoyin shiga Gaza, ta musanta cewa tana hana Shigar da kayan agaji da sauransu kai wa ga Falasdinawa fiye da su milyan 2 a Gaza. Kungiyoyin agaji na Falasdinu da kuma saura daga kasashen duniya duk sunce kayayyaki da suke isa Gaza sun gaza, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a cikin watan oktoban bara wadda a ciki aka bada tabbacin kara yawan kayayyakin masarufi da sauran su zuwa yankin.


