Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Muna Kokarin Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Gombe – Uwargidan Gwamna
Published: February 10, 2026 at 7:43 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: February 11, 2026

Uwargidan Gwamnan jihar Gombe, Hajiya Dakta Asma’u Inuwa Yahaya,ta jagoranci wani muhimmin taron wayar da kai da nufin ƙarfafa matakan dakilewa da kuma sauya ɗabi’un zamantakewa domin kawo ƙarshen cin zarafin mata da ‘yan mata.

An gudanar da taron ne a Cibiyar Ilimi wato (Education Resource Centre) da ke Tashan Dukku a birnin Gombe, tare da halartar jami’an gwamnati, shugabannin al’umma da na addini, ƙungiyoyin fararen hula, ƙungiyoyin mata, da kuma abokan hulɗar ci gaba.

Shirin, wanda aka aiwatar tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Matan Gwamnonin Nijeriya da kuma tallafin gidauniyar Ford Foundation, ya gudana ne ƙarƙashin taken: “Wayar da Kai don Rigakafi: Sauya Ka’idojin Zamantakewa da Ƙarfafa Ƙudurin Jiha Don Kawar da Cin Zarafin Mata.”

A jawabinta, Hajiya Dakta Asma’u Inuwa Yahaya Wacce Kwamishinar Ma’aikatar harkokin Mata Asma’u Mohammed Iganus ta wakilta ta jaddada cewa rigakafi shi ne hanya mafi tasiri wajen magance matsalar cin zarafi sannan ta bayyana cewa sauya tunani da halayen da ke goyon bayan danniya da take hakkin mata na da muhimmanci wajen gina al’umma mai adalci da mutunta juna.

Uwargidan Gwamnan ta kuma tabbatar da ƙudurin gwamnatin Jihar Gombe na ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su kare haƙƙin mata da ‘yan mata, tare da samar da ingantattun hanyoyin kai ƙorafi da tallafa wa waɗanda abin ya shafa.

Masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun yi kira ga haɗin kai tsakanin gwamnati, al’umma da ƙungiyoyin fararen hula domin tabbatar da cewa an kawo ƙarshen cin zarafin mata a kowane mataki. Sun kuma yabawa gwamnatin jihar bisa matakan da take ɗauka wajen ƙarfafa tsarin kariya da inganta walwalar mata da yara.

Taron ya kasance wani muhimmin mataki na ƙara wayar da kai da kuma gina aniyar haɗin gwiwa domin samar da al’umma mai zaman lafiya, adalci da mutunta haƙƙin bil’adama.

Ga Rahoton Aliyu Gerengi Gombe Daga Gombe

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/02/GBV-GOMBE.mp3
Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Majalisar Dattawar Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet
Next Post: Majalisar Dottijan Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Na’ura

Karin Labarai Masu Alaka

Tinubu Yace Zayyi Hadaka Da Kasashen Duniya Domin Kawo Karshen Rashin Tsaro. Najeriya
Eziekel Gomos Ya Zamo Babban Daraktan Sakatariyar Zauren Gwamnonin Arewa Najeriya
Jagoran Kwankwasiya A Najeriya Ya Koma Jam’iyar ADC Labarai
Za’a Jima Ana Fama Da Tsadar Farashin Mai Afrika
Anfara Gangamin Kafa Dokoki Masu Tsanani Ga ‘Yan Luwadi A Senegal Afrika
Isra’ila Ta Zantar Da Hukuncin Kisa Ga Masu Kai Hare Hare Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Usman Maiyama Ne Gwarzon Kamun Kifin Argungu Bana Labarai
  • Masana: ‘Yancin Kasashen Afrika A Rubuce Yake Ba A Zahirance Ba Najeriya
  • Shugaba Trump Yace Zai Dakatar Da Kai Hari Cibiyar Makamashin Iran Afrika
  • Kungiyoyi Sunyi Hasashen Jinkiri A Bunkasar Tattalin Arzikin Kashen Afirka Afrika
  • Trump Zai Sasanta Tsakanin Masar Da Habasha Amurka
  • Hukumar IMF Tana Naziri Domin Kara Bada Lamuni Ga Kasar Zambiya Afrika
  • Sama Da Zawiyya 100 Ne Suka Samu Tallafin Kayan Abinci Daga Al’mustapha Haji Sufi Labarai
  • Rwanda Tana Keta Yarjejeniyar Zaman Lafiya – Tshisekedi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.