Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • An Bawa Fasto Yohanna Buru Sarautar “Jagoran Zaman Lafiyar Arewacin Najeriya” Afrika
  • Inuwa Yahaya Ya Yi Alkawarin Barin Gombe Ba Tare Da Bashin Fansho Ba Afrika
  • NBA Gombe Ta Nemi IGP Ya Binciki Zargin Karɓar Kuɗi A FCID Annex Gombe Afrika
  • Ɗalibai 670 Sun Amfana Da Tallafin Jakakkuna Da Littattafai Daga Hukumar NEDC A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Gombe Ta Ƙarfafa Matakan Kare Dabbobi Daga Cututtuka Afrika

Pantami, Mailantarki Da Garry Za Su Fafata A Sabon Zaɓen Fidda Gwani Na PDP A Gombe
Published: September 25, 2026 at 6:01 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jam’iyyar PDP ta sanya ranar Talata, 29 ga Satumba 2026, domin gudanar da sabon zaɓen fid-da-gwani na takarar gwamnan jihar Gombe, bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke zaɓen da ya gabata wanda ya samar da Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar na zaɓen 2027.

Jam’iyyar PDP ta ɗauki matakin gudanar da sabon zaɓen fid-da-gwani ne bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe, wadda ta umarci jam’iyyar da ta sake gudanar da zaɓen bisa kundinta, ƙa’idojinta da dokokin zaɓe.

Mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta yanke hukuncin, bayan wani ƙara da ɗaya daga cikin masu neman tikitin gwamnan PDP, Usman Aliyu Garry, ya shigar yana ƙalubalantar tsarin da aka bi wajen fitar da Pantami.

A zaɓen da ya gabata a watan Mayun 2026, Pantami ya samu tikitin PDP ne ta hanyar amincewar murya, bayan ya koma jam’iyyar daga APC. Sai dai kotun ta soke tsarin tare da umartar PDP da ta gudanar da sabon zaɓen fid-da-gwani.

Rahotannin da suka fito ranar Juma’a sun ce PDP ta tantance Farfesa Isa Ali Pantami, Khamisu Ahmed Mailantarki da Usman Aliyu Garry domin shiga sabon zaɓen da aka sanya ranar Talata, 29 ga Satumba.

A baya, PDP ta bayyana cewa za ta mutunta hukuncin kotu tare da ɗaukar matakan da suka dace domin gudanar da sabon zaɓen cikin bin ƙa’idodin jam’iyyar da dokokin ƙasar.

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga mambobinta da masu ruwa da tsaki a Gombe da su kasance cikin nutsuwa, bin doka da haɗin kai yayin da ake kammala shirye-shiryen sabon zaɓen.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: ’Yan Sandan Bauchi Sun Kama Mutane Biyu Kan Zargin Kashe Jariri
Next Post: Gombe: An Kama Mutane Biyu Kan Zargin Kashe Matar Dan Sanda

Karin Labarai Masu Alaka

Majalisar Dokokin Filato Ta Kare Kudirin Alawus Ga Tsofaffin ‘Yan Majalisa Afrika
Shugaba Tinubu Yakarawa Mambobin ASUU Kashi 40 Na Albashi Najeriya
Kocin Zambia Na Mata Ba Lafiya Labarai
Majalisar Dattawar Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet Labarai
’Yan Sandan Bauchi Sun Kama Mutane Biyu Kan Zargin Kashe Jariri Afrika
Aisha Buhari Ta Bayyana Irin Kalubalen Da Ta Fiskanta Sakamakon Biyewa Jita-Jita Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • An Bawa Fasto Yohanna Buru Sarautar “Jagoran Zaman Lafiyar Arewacin Najeriya”
  • INEC TA Fitar Da Jerin ’Yan Takarar Gwamnan Gombe, Ba A Ga Sunan Sheikh Pantami Ba
  • Inuwa Yahaya Ya Yi Alkawarin Barin Gombe Ba Tare Da Bashin Fansho Ba
  • NBA Gombe Ta Nemi IGP Ya Binciki Zargin Karɓar Kuɗi A FCID Annex Gombe
  • Ɗalibai 670 Sun Amfana Da Tallafin Jakakkuna Da Littattafai Daga Hukumar NEDC A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jirgin Dakon Iskar Gas Daga Rasha Ya Sake Hanya Afrika
  • Tinubu Ya Kafa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Afrika
  • Shugaba Trump Ya Bukaci Kasar Iran Ta Mika Wuya Amurka
  • Farfesa Inuwa Ja’afaru Yakarbi Ragamar Shugabancin Jami’ar Kashere Labarai
  • Hotunan Hawan Sallah A Masarautar Bauchi Afrika
  • Gwamnan Jihar Filato Ya Karbi Katin APC Labarai
  • Hukumar Zaben Najeriya Ta Sanar Da Ranar Zaben Shugaban Kasa Labarai
  • Sarkin Musulmi Yayi Magana Game Da Matsalar Tsaron Kasar Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.