Ranar Alhamis, ofishin MDD mai kula da hakkin Bil’adama ya fitar da rahoto dake cewa an kashe fiye da farar hula 1000 lokacin da wata kungiyar mayakan wucin gadi a Sudan, da da karunta suka kwace iko a wani sansanin ‘yan gudun hijira a yankin Darfur cikin watan afrilun bana, kashi uku cikin wadanda aka hallaka an kashe su ne kai tsaye.
Watanni kafun ta kai farmakin daga 11-13 ga watan Afrilun, mayakan RSF sun hana kai abinci da wasu kayan agaji zuwa sansanin da ake kira zamzam a yammcin Darfur, inda mutane rabin milyan wadanda yaki ya tilastawa barin muhallensu suka sami mafaka, kamar yadda rahoton na MDD ya fada.
Wannnan rahoton sakamakon bincike ne da ya hada da magana da mutane 155 wadanda suka tsira daga harin da mayakan RSF suka kai kan sansanin, da wadanda aka yi abun akan idonsu, da ahalin yanzu suke Cadi zaman gudun hijira.
Daya daga cikinsu ya bada shaidan cewa an kashe mutane 8 da suka buya a cikin wani daki, yace dakarun RSF suka sa bakin bindiga suka harbe mutanen kamar yadda rahoton ya fada.
Ita dai RSF ta bada maida martani ba da ak nemi jin ta bakinta kan wannan rahoto.
Amma a baya ta musanta wannan zargi, tana cewa bata auna farar hula, kuma tana daukar mataki kan duk wani jami’inta da suke saba wannan doka.
Amurka da wasu suna kiraye kirayen a tsagaita wuta a wannan rikici na Sudan.


