Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Ribadu: Najeriya Ce Kasa Daya Tilo Da Ke Tabbatar Da Demokraɗiyya A Sahel
Published: December 4, 2025 at 8:58 PM | By: Yusuf Aliyu Harande

Mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya gargadi cewa dole ne a kare tsarin dimokraɗiyyar Najeriya, kasancewarta kasa daya tilo da take aiwatar da demokraɗiyya a duk yankin Sahel, inda rikice rikicen siyasa da juyin mulki suka yi kamari.

Ribadu ya yi wannan jawabi ne a Abuja, a wani taron tattaunawa kan rigakafi wanda Kwamitin Zaman Lafiyar Kasar, Cibiyar Kukah da Ofishin Mai bawa shugaban kasa shawara ta bangaren tsaro suka shirya.

Wannan gargadi nasa ya zo ne a daidai lokacin da juyin mulki ya yi katutu a kasashen yammacin Afirka da Sahel, kamar su Mali, Burkina Faso, Nijar da Chadi, inda aka sami hambarar da gwamnatoci.

Ribadu ya ce duk da kalubalen tsaro da na tattalin arziki da Najeriya ke fama da su, ita ce kadai kasa a yankin da har yanzu ke gudanar da mulkin farar hula bisa kundin tsarin mulki.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta samu hukuncin laifi 775 a kan masu aikata ta’addanci abin da ya ce alama ce ta ci gaban da ake samu sakamakon hadin kan hukumomin tsaro, al’umma da kuma bangaren shari’a.

Sai dai ya jaddada cewa wadannan nasarori na iya rushewa idan rikici, tashin hankali da rabuwar kai suka ci gaba da yawaita.

Ribadu ya kara da cewa ana iya samun zaman lafiya mai dorewa ne kawai idan tattaunawa ta rikide zuwa matakai na zahiri da za su kara karfin garkuwar al’umma, su dawo da amana, su kuma inganta tsaro a arewacin Najeriya.

Ya bayyana cewa yawancin matsalolin tsaro a kasa sukan fara ne daga matakin ƙananan hukumomi, yana mai jaddada muhimmancin rawar da al’umma, sarakunan gargajiya, malamai da gwamnatocin jihohi ke takawa wajen dakile rikici ya jadda da cewa idan aka bai wa al’umma damar magance matsalolinsu da kansu, buƙatar tura dakarun soja tana raguwa ƙwarai.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa, Bishop Matthew Kukah, ya ce matsalar tsaro ta taba kusan kowane dan Najeriya kai tsaye.

Bishop Kukah ya yi watsi da ra’ayin cewa al’umma su dauki makamai domin kare kansu, yana mai cewa daukar makami ba ya kawo tsaro na gaskiya, illa zai haifar da sabbin matsaloli a kasar.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Christ Musa Ministan Tsaro
Next Post: Kyaftin Na Super Eagles Ya Yi Ritaya.

Karin Labarai Masu Alaka

Tinubu: Abba Magajin Aminu Kano Ne A Fagen Siyasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Najeriya Ta Mika Koke Ga FIFA Tana Zargin DR Congo Ta Sanya ‘Yan Wasan Da Basu Cancantaba Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamnonin Arewa “Mun Amince Da Samar Da ‘Yan Sandan Jihohi” Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugaba Bola Tinubu Ya Tafi Turai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Aliko Dangote: Faruk Ahmed Ya Ci Amanar ‘Yan Najeriya! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Jihohin Arewaci Sun Kafa Asusun Yaki Da Ta’addanci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Kasar Zimbabwe Ta Samar Da Dokar Tsawaita Mulkin Mnangagwa Zuwa 2030
  • ‘Yan Bindiga Sun Karya Alkawarin Dakatar Da Kai Hare Hare A Najeriya
  • Amurka Zata Bawa Sojojin Najeriya Horo
  • Indonesia Zata Kafafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Gaza
  • Shugabannin Kasar Australia Sun Bukaci ‘Yan Kasar Suyi Zanga Zanga Cikin Lumana

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ganduje Ne Yasa Aka Kama Ni Inji Muhuyi Magaji Najeriya
  • Shugaban Najeriya Bola Tinubu Zai Ziyarci Jihohin Borno,Bauchi Da Legas Labarai
  • An Sace Masu Ibada A Wata Majami’ar Ecwa A Jihar Kogi Tsaro
  • A Kowacce Rana Kasar China Tana Sayan Danyen Mai Ganga Dubu 600 Daga Kasar Venezuela Amurka
  • An Kashe Mutane 7 A Unguwar Dorayi Dake Kano Najeriya
  • Iran Ta Kama Wani Jirgin Ruwa Shake Da Mai Labarai
  • Sojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Bindiga A Kano Da Katsina Tsaro
  • Kasashen Turai: Bazamu Yarda Da Dokar Harajin Trump Ba Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.