Shaidun gani da ido, da ma’aikatan agaji da kuma kwararru sun yi zargin cewa rundunar sojojin wucin gadi ta RSF ta kasar Sudan, tana yin garkuwa da mazauna wuraren da ta kama a yankin Darfur tana neman sai ‘yan’uwansu sun biya diyya kafin ta sake su.
Shaidun suka ce wadanda suka kasa biya, ana kashe su, ko a lakkada musu mummunar duka.
Babu tabbas na yawan mutanen da rundunar ta RSF take rike da su a bayan da ta kama al-Fasher, babban birnin Darfur ta Arewa a karshen watan Oktoba, amma an ce ana tsare da su a wurare dabam-dabam a sansanoni da kauyuka da dama dake yanki mai fadin kilomita 80 daga birnin, yayin da wasu ma an maida su cikin al-Fasher ana neman dubban daloli daga hannun ‘yan’uwansu.
Wadanda suka tsira da yawa da suka yi hira da Reuters sun ce ana tilasta ma ‘yan’uwanssu biyan abinda ya kama daga Fam miliyan 5 zuwa fam miliyan 60 na kudin kasar Sudan, kimanin Naira miliyan biyu zuwa miliyan 25 a kudin Najeriya, kafin a sake su, wanda kudi ne mai tsananin yawa a wannan kasa mai fama da talauci.
Wasu shaidu su 11 sun ce wadanda suka kasa biya, ana tattara su a bindige, ko a yi musu mummunar duka. Wani da ya iya samu ya biya ya kubutar da kansa, Mohammed Isma’ila, ya ce ana ba mutum kwana uku ko hudu, idan har ba a aika musu da kudin ba, sai su kashe mutum.
Yace shi da wani dan’uwansa sun tsere daga al_Fasher, amma dakarun RSF suka kama su a wani kauye kuma kowannensu sai da ya biya fam miliyan 10 na kudin Sudan, kimanin Naira miliyan hurhudu, kafin aka sake su.
Da aka nemi jin ta bakinsa, mai ba rundunar RSF shawara kan harkokin shari’a, Mohammed Mukhtar yace, wata kungiya mai adawa da tasu ce da take shigar burtu a matsayin RSF take gudanar da akasarin wannan aiki na kama mutane don neman kudin fansa a ciki da wajen birnin al-Fasher.


