Rundunar Sojin Saman Najeriya ta Bayyana cewa Jirgin ta yana kan hanyar zuwa Portugal ne ba aikin leken asiri ba.
Rundunar sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta tabbatar da cewa jirginta kirar C-130, wanda aka tilasta sauka a Burkina Faso, na kan aikin jigilar jirgi zuwa ƙasar Portugal ne ba wani aikin ɓoye ko sirri ba.
Mai magana da yawun NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana cewa membobin tawagar sun lura da matsalar na’ura bayan tashin jirgin daga Legas, wanda hakan ya sa sukar gaggawa a Bobo Dioulasso abin da ya kira da ka’idar tsaro ta duniya a zirga-zirgar jirage.
Wannan bayani ya fito ne bayan da ƙungiyar Alliance of Sahel States (AES) ta zargi jirgin da karya dokar sararin samaniyarsu, tare da barazanar shugaban juyin mulkin Mali, Assimi Goïta, da cewa duk wani jirgi da bai da izini yasauka a yankin.
Hukumar NAF ta kara da cewa dukkan jami’ai 11 da ke cikin jirgin na cikin koshin lafiya kuma ana kula da su yadda ya kamata,


