Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • REAL MADRID: VALVERDE YA SAMU RAUNI MAI TSANANI A ƘAFA Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15 Afrika
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe Afrika
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya Afrika
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu Kiwon Lafiya

Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Kuɓutar da Yaro Daga Hannun Masu Garkuwa
Published: July 2, 2026 at 9:43 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya ta sanar da ceto wani yaro mai shekara takwas da aka sace, tare da kama mutum huɗu da ake zargi da hannu wajen aikata laifin.

A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, an fara bincike ne bayan iyalan yaron sun kai rahoton ɓacewarsa ga ‘yan sanda a Ƙaramar Hukumar Akko.

Binciken da jami’an tsaro suka gudanar ya kai ga cafke wani da ake zargi a Kumo, wanda daga bisani ya taimaka wajen kamo wasu mutum uku da ake zargi da haɗa baki wajen sace yaron.

Rundunar ta ce an gano yaron a hannun waɗanda ake zargin, inda aka ceto shi cikin ƙoshin lafiya ba tare da ya samu wani rauni ba, sannan aka miƙa shi ga iyalansa.

‘Yan sandan sun bayyana cewa bincike kan lamarin na ci gaba, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya yaba da ƙwarewar jami’an da suka gudanar da aikin, tare da yin kira ga jama’a su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaƙi da aikata laifuka.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Tinubu Ya Buɗe Katafaren Kamfanin Sarrafa Lithium Domin Bunƙasa Tattalin Arziki
Next Post: Jana’izar Jagoran Ƙolin Iran Ta Kawo Tsauraran Matakan Tsaro A Tehran

Karin Labarai Masu Alaka

Kamfanin Mai Na NNPC Yasamu Gwaggwabar Riba Labarai
Shugaban Amurka Donald Trump Yace Amurka Zata Kai Babban Farmaki Iran Afrika
Borno: An Yi Kwanton Bauna Kan Ayarin Ɗan Takarar Gwamna Afrika
Farashin Mai Ya Doshi Dala 100 Kowacce Ganga Afrika
Amurka Zata Aika Jiragen Yaki Biyu Gabas Ta Tsakiya Amurka
Bayan Rikicin Manoma Da Makiyaya, Kwamitin White Paper Ya Ziyarci Bojude Da Kwami Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • REAL MADRID: VALVERDE YA SAMU RAUNI MAI TSANANI A ƘAFA
  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe Afrika
  • Muna Kokarin Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Gombe – Uwargidan Gwamna Labarai
  • Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Roger Lumbala Shekaru 30 Labarai
  • Isra’ila Ta Zantar Da Hukuncin Kisa Ga Masu Kai Hare Hare Labarai
  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna Afrika
  • Gwamnatin Jihar Filato Ta Sauke Hakimin Mushere Afrika
  • Turkiyya Tana Gudanar Da Binciken Kasar Da Suka Kona Tutar Ta Tsaro
  • Sojoji Sunkai Farmaki Gidan Dan Adawa A Kasar Uganda Bobi Wine Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.