Mutumin nan da ya kai hari ya kashe Amurkawa uku, sojoji biyu da tafinta daya, a kasar Sham, bai jima da shiga aikin tsaro a kasar ba, inda watanni biyu da suka shige hukumar tsaron cikin gida ta kasar Sham ta dauke shi aiki a zaman mai gadi a wani sansanin soja.
Amma da aka fara damuwa da halayyarsa, sai aka fara zargin cewa yana da alaka da kungiyar ISIS, don haka aka sauya mishi wurin aiki.
Harin da ya kai a kusa da kangon birni mai tarihi na zamanin da, Tadmur, ko Palmyra da turanci, ya kuma raunata wasu mutane 3.
Kakakin ma’aikatar harkokin ckin gida ta Sham, Nour al-Din al Baba, yace dakarun tsaron Sham guda uku ma sun ji rauni a bayan da suka yi musayar wuta da dan bindigar.
Kakakin yace sun fuskanci karancin jami’an tsaro saboda yadda gwamnati ta fado hannunsu haka kwatsam, kuma dan bindigar yana daga cikin mutane dubu 5 da aka dauka cikin wata sabuwar runduna da aka kafa ta tsaron cikin gida.


