Samar da man fetur a ƙasar Iraq ya ragu matuƙa yayin da yakin Iran ke ci gaba da ƙamari, inda tankunan ajiyar mai suka cika har matakan haɗari, a daidai lokacin da ƙasar ba ta iya fitar da danyen mai ta mashigar Strait of Hormuz, kamar yadda jami’an makamashi uku na Iraq suka bayyana a ranar Laraba.
Jami’an sun ƙara da cewa samar da mai daga manyan filayen man fetur na kudancin ƙasar ya ƙara raguwa da kusan kashi 80 cikin ɗari, inda ya sauka zuwa kimanin ganga 800,000 a kowace rana.
A farkon wannan watan, samar da man fetur daga waɗannan manyan filaye na kudanci ya riga ya ragu da kusan kashi 70 cikin ɗari zuwa kusan ganga miliyan 1.3 a kowace rana, sakamakon rashin damar fitar da mai ta mashigar Hormuz, kamar yadda majiyoyin masana’antu suka bayyana.
Kafin barkewar yakin, yawan samar da mai daga filayen ya kai kusan ganga miliyan 4.3 a kowace rana.
Jami’an sun ce Iraq ta yanke shawarar ƙara rage samar da mai tun daga ranar Talata, bayan ta bukaci kamfanin BP ya rage yawan samar da mai daga babbar rijiyar Rumaila da ganga 100,000 a kowace rana, wanda hakan ya saukar da samarwa zuwa kusan ganga 350,000 daga kimanin ganga 450,000 a baya.


