An kama wani Mutum da ake zargi ɗan damfara ne da yake zaluntar masu jinya a Asibiti ATBUTH Bauchi
Wata takarda da aka rabawa manema labarai ya tabbatar da cewa sashen SERVICOM na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke tarayyar Najeriya a jihar Bauchi, ya danke wani mani Mutum da ake zargin ɗan damfara ne da yake damfarar wadda suka zo jinya a asibitin da danginsu a cikin haraba.
Bayanan na cewar an kama mutumin ne a lokacin wani aikin surru da akayi cikin dare kamar yadda aka saba yi a wasu lokuta, inda aka same wadda ake zargin ya karbi naira dubu 45, daga dangin wani majinyaci da yake samun kulawa sakamakon raunin harbin bindiga.

A cewar sanarwar dauke da sahanun Jami’in Hulda da Jama’a na ATBUTH, Usman Abdullahi Koli tace wanda ake zargin ya nemi a bashi Naira 5,000, a matsayin kuɗin katin asibiti sai kuma Naira 40,000, don sayan magunguna.
Koli, yace ainihin kudin katin asibitin Naira 1,000, ne yayin da kuɗin magungunan suka kai Naira 18,150.
Sai dai an karɓi sauran Naira 27,000 daga hannun wanda ake zargin, inda daga bisani aka mika shi ga hukumar ‘yan sanda don cigaba da bincike da kuma gurfanar da shi a gaban shari’a.

Da yake tsokaci dangane da wannan faruwar wannan lamarin, Shugaban asibitin ATBUTH, Farfesa Yusuf Jibrin Bara, ya yaba wa tawagar ta SERVICOM bisa kokarin su na gano wannan mumunar barnan da kuma sanya ido da suka yi, daga bisani ya sake nanata manufar hukumar asibitin na yaƙi da cin hanci da zamba, kutse a aikin jami’a, da sauran munanan ayyuka.
Inda ya bukaci marasa lafiya da jama’a da su kasance masu lura da al’uman da zasu zo musu da niyar zasu taimakesu, da su gaggauta kai rahoton duk mutanen da basu yarda da shi ba, ko kuma bukatar biyan kudi ba bisa ka’ida ba zuwa ofishin SERVICOM ko su nemi hukumomin asibiti.
Farfesa Bara ya ce yana mai tabbatar da cewa hukumar gudanarwa za ta ci gaba da karfafa hanyoyin sa ido don kare majinyanta da tabbatar da gaskiya a asibitin.


