Shahararren ɗan dambe a duniya, Anthony Joshua, ya yi haɗarin mota a Makun, Jihar Ogun.
Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne a kan wata babbar hanya mai cunkoso a kan titn Lagos–Ibadan Expressway.
Motar da ke dauke da Joshua, wata motar Lexus Jeep mai lambar mota, KRD 850 HN, ta yi karo da wata babbar mota da ke tsaye a wani yanayi da har yanzu ana ci gaba da bincike.
An ruwaito cewa dan damben ya samu kananan raunuka, yayin da wasu mutane biyu suka mutu nan take.
Ana fargabar an samu asarar rayuka yayin hatsarin.



