Shugaban Najeriya Bola Tinubu a ranar Alhamis ya ƙara jaddada ƙudurin sa na kafa ’yan sandan jihohi, inda ya bayyana cewa ya ba wa Amurka da abokan hulɗan Turai tabbacin cewa zai aiwatar da tsarin ’yan sandan jihohi a Najeriya.
Ya jaddada cewa dole ne a kafa ’yan sandan jihohi “ba tare da ja da baya ba” a matsayin wani muhimmin mataki na inganta tsaron cikin gida da ƙarfafa tsarin mulki a matakin jihohi.
Tinubu ya faɗi hakan ne a taron ƙungiyar manyan jiga-jigan APC karo na 14 da aka gudanar a Cibiyar Taron Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja.
A wajen taron, ya kuma dage cewa ’dole ne aiwatar da hukuncin cin gashin kan Kananan hukumomi a aikace, inda ya buƙaci gwamnonin jihohi da su daina riƙe kuɗaɗen da aka ware wa shugabannin ƙananan hukumomi.
Jawaban Shugaban Ƙasa sun zo ne a daidai lokacin da matsalolin tsaro ke ƙaruwa a faɗin ƙasar, tare da sabbin kiraye-kirayen neman kafa’yan sandan Jihohi, da kuma ƙoƙarin aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli kan ’yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi da kuma raba musu kuɗi kai tsaye.
Tinubu ya shawarci shugabannin jam’iyya cewa APC, a matsayin ta na jam’iyya mai rinjaye, dole ne ta nuna jagoranci ta hanyar sasantawa, fahimtar juna da sassauci a matakin ƙasa, yana kuma ƙarfafa gwamnonin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki da su ɗauki alhakin abin da ke faruwa a jihohin su da ƙananan hukumomin su.
Ya ce kwanan nan ya tattauna da abokan hulɗa na ƙasashen waje, inda ya tabbatar musu da cewa Najeriya za ta tunkari tsarin ’yan sandan jihohi, yana mai ƙarawa da cewa yana da tabbacin jam’iyyar APC za ta bayar da cikakken goyon baya.
Yakara da cewa,“Na yi doguwar tattaunawa da su abokan hulɗa daga Amurka da Tura kuma na faɗa musu cikin alfahari cewa tabbas za mu zantas da dokar ’yan sandan jihohi domin inganta tsaro.”


