Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bar birnin Lagos a ranar Lahadi, 28 ga Disamba, domin ci gaba da hutun karshen shekara a Turai, kafin daga bisani ya wuce Abu Dhabi a Hadaddiyar Daular Larabawa.
An gayyaci Shugaba Tinubu ne don ya halarci taron Abu Dhabi Sustainability Week 2026, wanda ake shirin gudanarwa a farkon watan Janairu, inda manyan shugabanni daga bangaren gwamnati, ‘yan kasuwanci ke tattauna hanyoyin bunkasa ci gaba mai dorewa a duniya.
A cikin wata sanarwa da Mai bai wa Shugaban Nijeriya shawara na musamman kan yada labarai Mr. Bayo Onanuga, ya fitar, ta bayyana cewa Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, shugaban hadaddiyar Daular Larabawa, ne ya gayyaci Shugaba Tinubu domin halartar taron.
Sanarwar ta ce shugaban kasar zai dawo Nijeriya da zarar an kammala taron UAE din.


