Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Shugaba Tinubu Ya Taya Musulmai Murnar Sallah, Tare Da Kira Zuwa Ga Kishin Kasa
Published: March 19, 2026 at 9:30 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaba Tinubu ya taya Musulmi murnar Sallah, tare da kira zuwa ga kishin ƙasa

Shugaban ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya al’ummar Musulmi murnar Sallar Ƙaramar Idi (Eid-el-Fitr), tare da kira ga su ƙara jajircewa wajen hidimtawa ƙasa da al’umma baki ɗaya.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, shugaban ya bukaci Musulmi su ci gaba da riƙe darussan watan Ramadan, musamman waɗanda suka shafi tsoron Allah, tausayi da haɗin kai tsakanin al’umma.

Ya ce akwai darussa masu yawa da ya kamata a ɗauka daga Ramadan, musamman a irin wannan lokaci, yana mai jaddada muhimmancin bin kyawawan halaye kamar sadaukarwa, juriya, alheri da jin ƙai har bayan watan azumi.

Shugaban ya kuma buƙaci Musulmi su miƙa taimako ga masu buƙata ba tare da la’akari da addini ba, domin ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakanin ‘yan ƙasa.

Haka zalika, ya roƙi shugabannin addini su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa ƙasa addu’o’in zaman lafiya da ci gaba.

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin za ta ci gaba da ƙoƙarin samar da yanayi mai kyau domin walwalar al’umma.

Afrika, Labarai, Najeriya, Nishadi

Post navigation

Previous Post: Ambaliyar Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutum 13 A Malawi
Next Post: Isra’ila Tace Bazata Sake Kai Hari Kan Cibiyar Gas Ta Iran Ba

Karin Labarai Masu Alaka

Yohanna YD Buru: Makon Haɗin Kan Addinai Ya Ƙarfafa Ilimin Zaman Lafiya A Najeriya Labarai
Tsohuwar Ministan Albarkatun Mai Ta Bayyana A Kotu Najeriya
Dangote Ya Rage Farashin Mai A Najeriya Labarai
Sarkin Musulmi Ya Ziyarci Shugaba Bola Tinubu Afrika
Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki Labarai
Dalibin Jami’a Ya Rasa Ransa A Birnin Dakar Yayin Zanga Zanga Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Isa Legas Domin Hutun Karshen Shekara Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Guinea Bissau Ta Tsaida Gwaje-Gwajen Allurar Rigakafin Shawara A Kasar Labarai
  • APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya Najeriya
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu Wasanni
  • Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Ranakun Hutu Najeriya
  • ECOWAS Da AU Sun Nuna Damuwa Kan Juyin Mulki A Guinea-Bissau Afrika
  • Hamas Ta Kwance Damara Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.