Shugaban Amurka Donald Trump ya dage kai hare-hare cibiyar wutar lantarki ta Iran. Trump yace jakadun sa biyu sun tattauna da wani jagora na Iran da ake ganin girman sa. Ya kara da cewa akwai dama sosai ta cimma yarjejeniya. Iran kuma a nata bangaren ta musanta cewa an gudanar da wata tattaunawa.
Farashin man fetur ya fadi, yayin da aka samu riba a kasuwannin hannun jari saboda dage kai hari ga cibiyar wutar lantarkin Iran da Amurka ta yi.
Iran ta dau alwashin kai hari kan ababan more rayuwa na yankunan Gulf idan har Amurka ta kai harin kan cibiyar wutar lantarkin ta.


