Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Shugaban Amurka Yace Zayyi Wahala A Cimma Yarjejeniya Tsakanin Isra’ila, Amurka Da Iran
Published: March 27, 2026 at 6:26 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Amurka Donlad Trump ya ce ‘yan kasar Iran, mutane ne da suka kware wajen tattaunawa kan cimma yarjejeniya, amma ya kara da cewa baya zaton zai yi wata yarjejeniya da su don kawo karshen yakin da Isra’ila da Amurka suke yi da Iran din.

Da yake magana yayin wata tattaunawa da majalisar ministoci a fadar White house, Trum yace yanzu Iran na da damar soke duk wani kudiri nasu na makamashin nukiliya har abada, su sauya manufa. Ya kara da cewa zamu ga idan suna so suyi hakan, idan kuma sun ki, zamu zame musu karfen kafa, mu ci gaba da aika musu da bama bamai.

Jawabin na Trump yayi biyo bayan matsin rayuwa da sanadin yakin ya jawo ke kara tsamari, inda ake fuskantar rashin isasshen man fetur da gas, abinda ya sa kamfanoni da kasashe tashi tsaye wajen kokarin shawo kan lamarin.

Jakadan Amurka na musamman, Steve Witkoff ya tabbatar da cewa Amurka ta aike da takarda mai dauke da ka’idoji 15, a matsayin hanyar da za’a bi don tattaunawa kan kawo karshen yakin, ya kara da cewa akwai alama cewa fadar gwamnatin Tehran nada sha’awar cimma yarjejeniya.

Ministan harkokin waje na kasar Pakistan yace tattaunawa tsakanin Amurka da iran na wanzuwa ne ta hanyar sakonni da ake aikowa ta hannun fadar gwamnatin Islamabad, tare da wasu kasashe da suka hada da Turkiyya da Masar, wanda suma suke goyon bayan tattaunawar sulhu.

Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Wani Jami’in Iran Yace Amurka Taso Kanta A Tattaunawar Tsagaita Wuta
Next Post: Isra’ila Ta Cire Sunayen Wasu Mutane Biyu Cikin Wadanda Take Fako

Karin Labarai Masu Alaka

Hotunan Hawan Sallah A Masarautar Bauchi Afrika
Amurka Zata Bada Gudumawar Kudi Dala Bilyan 10 Ga Ayyukan Kwamitin Wanzar Da Zaman Lafiyan Amurka
Kasar Canada Ta Amince A Shigar Da Motoci Kirar Kasar China Kasar Amurka
Tsohon Lauyan Amurka Jack Smith Ya Fadi Maganganu Game Da Donald Trump Amurka
Trump: Isra’ila Ta Daina Kai Hari Ga Duk Cibiyar Iskar Gas Afrika
Kungiyar MDD Ta Bukaci Ayi Bincike Game Da Kashe ‘Yan Iran Sauran Duniya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hari Akan Wata Mashaya Ya Rutsa Da Mutane 9 A Afirka Ta Kudu Afrika
  • An Kai Hari Da Jirgi Mara Matuki A Kusa Da Matatar Mai Din Kasar Sundan Afrika
  • Wakilan Rasha Da Ukraine Sun Tattauna A Abu Dhabi Ranar Juma’a Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kotu A Birnin Tarayya Abuja Ta Bada Belin Tsohon Minista Abubakar Malami Najeriya
  • Libya Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasashen Faransa Da Amurka Afrika
  • Kasar China Ta Kaddamar Da Rawar Daji A Yankin Taiwan Labarai
  • Hawan Sallah A Jihar Katsina Afrika
  • Hukumar Hisbah Ta Kona Barasar Dubban Nairori A Katsina Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.