Shugaban Amurka Donald Trump yayi barazanar kulle dan jaridar da ya fara yada rahoton cewa Dakaru na neman sojan jirgin Amurka F-15 da Iran ta kado.
Trump bai fadi sunan dan jaridar ba, ko kuma kafar yada labaran da yake wa aiki. Ya ce rahoton zai iya sanarwa da Iran me ake ciki, ya saka sojan da dakarun da ke kokarin kubutar da shi cikin hadari.
Trump ya fadi haka ne lokacin wani taron manema labarai a yau Litinin, inda ya ki amincewa da kudurin da Iran ta gabatar na kawo karshen yakin da suke tafkawa.


